in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dakatar da shawarwarin zaman lafiya na Syria
2016-02-04 10:27:32 cri

Jiya Laraba ne zaman shawarwarin shimfida zaman lafiyar Syria dake gudana a birni Geneva ya gamu da matsala, inda a daren wannan rana, ba zato ba tsamani, manzon musamman na MDD kan batun Syria Staffan De Mistura, ya sanar da dage gudanar da shawarwarin zaman lafiya na wannan zagaye, inda ya ce, za a ci gaba da zaman a ranar 25 ga wannan wata. De Mistura ya yi ganawa da manema labarai, inda ya sanar da cewa, za a dakatar da gudanar da shawarwarin zaman lafiya kan batun Syria wanda aka fara a Geneva, saboda bai wa bangarori daban daban da abin ya shafa lokacin kara yin sulhu tsakanin su.

De Mistura ya bayyana cewa, "Tun daga rana ta farko, na nuna cewa, ba na son a ce shawarwari kawai za a gudanar, a maimakon haka ina fatan a samu sakamako. Babban sakataren MDD Ban Ki-moon shi ma ya taba fadar hakan. Al'ummar Syria sun fi mai da hankali kan halin jin kai da suke ciki, kuma sun fi mai da hankali kan hakikanin sakamakon da za a samu. Shi ya sa muka tsai da kudurin dakatar da shawarwarin na dan gajeren lokaci, za mu ci gaba da gudanar da su. Kuma wannan ba ya nuna cewa, kokarinmu ya bi ruwa. Saboda me? Duka bangarorin sun zo, kuma bangarorin sun amince da wata matsaya guda, wato suna fatan ganin an cimma burin shimfida zaman lafiya ta hanyar siyasa, saboda haka na tsai da kuduri cewa, za mu ci gaba da yin shawarwarin zaman lafiya kan batun Syria a ranar 25 ga wannan wata."

De Mistura ya jaddada cewa, idan an gaza samun hakikanin sakamakon da zai amfani al'ummar Syria, to, shawarwarin ba su da ma'ana ko kadan. Ya ci gaba da cewa, kawo yanzu an tabbatar da cewa, an riga an fara gudanar da shawarwarin zaman lafiyar Syria a hukumance. Gwamnatin Syria da rukunonin 'yan adawar kasar sun tura tawagoginsu, kuma sun nuna ra'ayoyinsu. Duk da haka, ana bukatar lokaci domin daidaita wasu matsalolin dake gabansu.

Game da sabon zagaye na shawarwarin zaman lafiyar da za a yi, De Mistura ya nuna fatan alherinsa yana cewa, "Abun dake gabanmu shi ne, ko za mu sake gudanar da wani taro a Geneva kadai, ko kuma za mu yi la'akari sosai kan abun da muka fada. Ina fatan yayin da muke sake yin shawarwarin, za mu gabatar da batutuwan da suke shafar makomar Syria, da sabon tsarin mulkin Syria, da sabon babban zaben kasar, saboda al'ummar Syria suna sa ran za mu samu sakamako mai yakini."

Kawo yanzu, an sauya manzon musamman na MDD kan batun Syria har sau uku, a bayyane ta ke cewa aikin da suke gudanar wa yana da wahala. De Mistura shi ma yana aiki ne a birnin Geneva ba dare ba rana. Game da halin da ake ciki a Geneva, De Mistura ya ce, bai yi bakin ciki ba. Ya ce, "Raina bai bace ba, kuma ban yi bakin ciki ba, tsawon lokaci, ni da MDD mun gane sosai cewa, kasar Syria ta sha wahalhalun yake-yake a cikin shekaru biyar da suka gabata, dole mu sa niyyar daukar hakikanin matakai na cimma burin shimfida zaman lafiya a kasar. Yanzu muna yin iyakacin kokarin gudanar da shawarwarin zaman lafiya, muna fatan za a samu sakamako mai gamsarwa. Idan mun gamu da wahala, to, ya kamata mu kara yin kokari, wannan aiki ne da muke yi yanzu."

Daga bisani, tawagar wakilan rukunonin 'yan adawar Syria ita ma ta gaya wa manema labarai cewa, idan gwamnatin Syria ba ta daina kai musu hari ba, kuma ba a kyautata halin jin kai da ake ciki a kasar ba, to, ba zai yiwu su koma teburin shawarwari ba. Kawo yanzu dai tawagar gwamnatin Syria, ba ta nuna ra'ayinta game da hakan ba. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China