in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Sin sun kara bullo da matakan sakarwa kasuwa mara
2016-02-04 16:48:33 cri

Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta sake fito da wasu matakan rage ikon hukumomin gwamnati don mayar da su ga hannu al'umma da matakan yin gyare-gyare, ta yadda za a kara sakarwa kasuwa mara.

Majalisar ta dauki wadannan matakai ne a zaman da ta yi na ranar 13 ga watan Janairun shekara ta 2016. Yanzu haka fiye da matakan iko 150 ne wannan mataki zai shafa a shekarar da muke ciki, ciki har da soke ikon neman izinin biya kudin haraji, ikon duba takardun neman izinin sayar da basussukan kamfanoni na kananan hukumomi kafin su sayar da su. Sannan an soke wasu ka'doji fiye da goma wadanda suke kawo cikas ga kokarin kafa sabbin kamfanoni da kirkiro sabbin fasahohin zamani. Sai dai za a sake kyautata matakan ba da hidima saboda wasu dilalai.

Masu sharhi na ganin cewa, wannan mataki zai taimaka a kokarin da kasar ke yi na zurfafa gyare-gyare da bunkasa tattalin arzikin kasar. Sannan wata dama ce ta bullo da fasahohi da kara samar da kudaden shiga ga jama'a.

Wani babban albishir ga wadannan matakai da mahukuntan kasar ta Sin suka dauka, shi ne samar da karin guraben ayyukan yi musamman ga matasa. Har ila matakan za su kara bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da sauran kasashe.

Masana sun yi imanin cewa, mudidin masu sha'awar kafa masana'antu ko tafiyar da wasu nau'o'in kasuwanci a kasar Sin na cikin gida da waje suka martaba dukkan tanade-tanaden da ke kunshe cikin wadannan tsare-tsare, babu tantama za su ci gajiyar wannan dama. (Ibrahim,Mamane Ada, Saminu, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China