in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarin rukunin kwararru a fannin gona na kasar Sin da ke tallafawa kasar Senegal wajen kawar da talauci
2016-02-03 14:36:26 cri

A cibiyar ba da horo ta Sangai-lekamu da ke yankin karkara a Dakar babban birnin kasar Senegal, akwai wasu Sinawa da suke kokarin samar da fasahohin da suka samu wajen shuke-shuken kayan lambu, da samar da ire-iren kayan lambu, don taimaka ma mazauna iya kyautata ingancin kayan lambu, da kara kudin shigarsu, da kuma samun wadata. Wadannan Sinawa kwararru ne a fannin aikin gona dake tallafawa kasar Senegal.

A watan Janairu, a kasar Senegal, ana samun hasken rana sosai, kamar yadda a kan yi a kullum, kwararrun a fannin aikin gona na kasar Sin Tan Bing da Yuan Junquan su kan sammako don fara gudanar da aiki. A gidan shuke-shuken kayan lambu na cibiyar ba da horo ta Sangai-Lekamu da fadinta ya kai eka 1.5, a kan noma kayan lambu iri iri sama da 20. Da karfe 7 na safiyar ko wace rana, Tan Bing da Yuan Junquan kan yi sintiri a gonakin kayan lambu, don duba yanayin da ake ciki. Bayan da suka duba gonaki da taki, idan suka gano wasu matsaloli, za su nuna wa ma'aikatan wajen nan take, don su gyara. Idan suka gamu da wasu matsaloli cikin sauki, za su iya kwatantawa da hannu da yin wasu bayani game da wasu kalmomi na Faransanci, wanda 'yan kasar za su gane. Yayin da suka gamu da wasu matsaloli na sarkakkiya, mai aikin tafinta Wang Xinxing sai ya shiga aikin sa, don kara fahimtar juna tsakaninsu.

Bisa labarin da shugaban rukunin aikin gona na kasar Sin Zheng Junjie ya bayar, an ce, a cibiyar ba da horo ta Sangai-Lekamu, akwai ma'aikatan kasar Senegal 18 da suka yi shuke-shuken kayan lambu, kwararrun kasar Sin sun dauki nauyin ba da horo, da nuna fasahohi. Ban da wasu ma'aikata 4 da suka gudanar da aiki cikin dogon lokaci, ragowar mutane 4 sun kasance manoman da suka zo cibiyar don koyon fasahohin kayan lambu da kansu, bayan da aka sayar da kayan lambu , ban da wasu kayan masarufi, za a yi amfani da sauran kudade don biya albashin ma'aikata.

Zheng Junjie ya ce, ban da daukar wasu masu aikin sa kai a dakin shuke-shuken kayan lambu na cibiyar, an kuma gudanar da wasu kwas din ba da horo, da kara yawan masu ilimi. A shekarar 2015 kawai, wannan rukuni ya yi hadin gwiwa da bangaren soji na kasar Senegal, don koyar da kwas har sau biyar ga sojoji, yawan daliban da suka shiga cikin kwas ya kai 159. Haka kuma, rukunin aikin gona ya kafa sansanonin nune-nunen shuke-shuken kayan lambu 15 a wuraren da ke kewaye da wurin, kuma su kan nace kan sintiri sau 2 a ko wane mako, don warware matsalolin fasahohi da manoma su kan gamu da su yayin da suka noma, kana su kan ba da tallafi game da wasu kayayyaki.

A karkashin taimako daga rukunin aikin gona, wasu manoman Senegal sun zama masu wadata. Diyallo mai shekaru 54 ya kasance daya daga cikinsu. Ya ce, kafin rukunin kwararrun kasar Sin su isa nan, ya kan noma kamar yadda ya yi a lokacin da, amma ba a iya samun kayan lambu masu yawa ba. Wata rana, bayan da ya ji labarin kwararru Sinawa, sai ya nemi shawara daga wajensu, bayan da ya je wurin da rukunin kwararrun suke da zama, ya gaya musu fatansa na koyon fasahohi, inda rukunin kwararrun suka karbe shi da hannu biyu-biyu, abin da ya sa ya zama daga cikin wadanda ke sha'awar fasahohin aikin gona na kasar Sin.

Diyallo ya ce, ya yi hadin gwiwa da Sinawa har na tsawon shekaru sama da goma, ya karu sosai kuma ban da fasahohi, rukunin kwararru Sinawa sun ba shi takin zamani da magungunan kashe kwari, da sauran kayayyaki, kana sun taimaka masa wajen kafa dakin shuken kayan lambu, abun da ya sa yawan kayan lambu da ya samu ya karu sosai, kuma kudin shiga da ya samu shi ma ya karu. A lokacin damini a kasar Senegal, bai dace da aikin gona ba, kuma a wancan lokaci, farashin kayan lambu yana da tsada kwarai, yayin da yawan kayan lambu da sauransu suka samu ya ragu, yawan kayan lambu da ya samu ya yi daidai, wannan shi ne babban canjin da fasahohin Sin ya kawo.

Bayan da fasahohi da kudin shiga ya karu, a watan Mayu na shekarar 2014, Diyallo ya kirkiro da wani sabon tunani, inda ya bar gonakinsa, bisa goron gayyata da abokansa suka yi masa, ya zama wani jami'in gonaki na abokansa. Masu gonaki sun dora muhimmanci sosai game da fasahohin da ya koya daga Sinawa. Diyyalo ya ce, yanzu, a cikin gonakin da fadinsa ya kai ekka 7, ya yi amfani da gonakin da fadinsa ya kai ekka 3 don shukan kayan lambu, ya yi amfani da ilmin da ya koya daga rukunin kwararru Sinawa, don gina dakin shuke-shuken kayan lambu na musamman. Game da makomar shuke-shuken kayan lambu, Diyyalo ya yi imani cewa, kwararrun kasar Sin su kan taimaka da wasu fasahohi sosai, duk lokacin da ya gamu da matsala, ya kan kira su, sannan kwararrun kasar Sin su kan zo nan, don taimaka masa, abun da ya karfafa zukatansa sosai.

Zheng Junjie ya ce, ko da yake, wani lokaci a kan fuskaci matsalar karancin mutane, amma, yayin da manoman wurin suke da bukatu sosai, su kan yi iyakacin kokarinsu, don biyan bukatun jama'ar wurin. A ranar 14 ga watan Satumbar shekarar 2015, rukunin kwararrun Sinawa sun tafi har na tsawon kilomita 240, don nuna wa wani manomi fasahohin shuke-shuke. Har ma, wani lokaci bisa goron gayyata da wakilan mata da matasa na lardin Tanbada dake da nisan kilomita 480 da Sangai Lekamu suka yi musu, sun shirya kwas guda 2 game da fasahohin shuke-shuken kayan lambu, da ya samu yawan daliban da suka halarta guda 103.

Fasahohin da rukunin kwararrun kasar Sin suka samu, ba ma kawai sun jawo hankalin manoman kasar Senegal ba, har ma wasu kungiyoyin kasa da kasa su ma sun dora muhimmanci sosai. A watan Mayu da watan Yuni na shekarar 2015, jami'an diplomasiyya na kasashen Asiya ciki har da na Koriya ta Kudu da Japan, da Thailand, da Malaysia da kwararru a fannin tattalin arziki na wakilin bankin duniya a kasar Senegal kimanin 30 sun ziyarci sansanin shuke-shuken kayan lambu da rukunin kwararrun Sin ya kafa, kuma sun jinjina ma aikin da suka yi. Ban da wannan kuma, a shekarar 2015, rukunin ya karbi ziyarar da mambobin kungiyar Better World na kasar Koriya ta Kudu suka yi, kana da mutane 11 daga kungiyar kawar da talauci na Mauritaniya-Hongkong da kungiyar daliban kasar Amurka.

Game da makomar raya rukunin, Zheng Junjie ya ce, rukunin kwararrun aikin gona zai ci gaba da gyare-gyare game da hanyoyin ba da horo, don kafa tsarin horar da jagora a fannin aikin gona daga duk fannoni, kana za su horar wa dalibai daga fasahohi da ilmi, don kara taimakawa Senegal samun wasu kwararru a fannin aikin gona.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China