160129-Sin-ta-sauke-nauyin-shiga-tsarin-gyare-gyare-kan-tattalin-arzikin-kasa-da-kasa-Lami.m4a
|
Tun daga rikicin hada-hadar kudi na duniya ya barke a shekarar 2008, an samu sauye-sauye da dama a kan tsarin tattalin arziki da hada-hadar kudi, a lokacin da raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wasu kasashe masu tasowa sun fuskanci kalubale a fannoni da dama musamman ma tattara kudade da kafa manyan kayayyakin more rayuwa, tsarin hada-hadar kudi na duniya na bukatar kyautatuwa sosai. A cikin wannan hali, an kafa bankin zuba jari kan aikin kafa manyan kayayyakin more rayuwa na Asiya.