160127-Tasirin-ziyarar-shugaban-kasar-Sin-a-yankin-gabas-ta-tsakiya-ga-ci-gaban-zaman-lafiya-a-duniya-Sanusi.m4a
|
Bayanai na nuna cewa, wannan ziyara ta tsawon kwanaki biyar ta kara tabbatar da kokarin da kasar Sin ke yi na tabbatar da zaman lafiya a duniya ta hanyar sabon shirin hadin gwiwar kasa da kasa na samun moriyar juna.
Ita ma kungiyar hada kan kasashen Larabawa wato AL a takaice, ta yaba da kokarin da kasar Sin take yi na taimakawa kasashe masu tasowa da matakan da mahukuntan kasar ke dauka na tabbatar da zaman lafiya da rashin tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe.
Masana na ganin cewa, ziyarar ta shugaba Xi Jinping a wadannan kasashe da a baya Amurka ta yi kane-kane, wata alama ce ta irin karbuwar da kasar Sin take kara samu a kasashen duniya.
Masu fashin baki na bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi zuwa yankin gabas ta tsakiya wadda ita ce ta farko a sabuwar shekara ta 2016, ta taimakawa shirin nan na "Ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi ya bullo da shi a shekarar 2013 kara samun karbuwa a yankin gabas ta tsakiya.
Idan ba a manta ba shugaban na Sin ya ziyarci kasashen Saudiya, Masar da Iran daga ranakun 18 zuwa 23 ga watan Janairun shekarar 2016, ziyarar da ta kara bayyana manufofin kasar Sin na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba. (Ibrahim/Sanusi Chen)