in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna anniyarta na rage hayaki mai gurbata muhalli da tsimin makamashi
2016-01-26 13:42:42 cri
Mataimakin ministan kula da makamashin Amurka Jonathan Elkind ya bayyana cewa, a matsayin wata babbar kasa mai tasowa a kasashen duniya, da kasar da ta fitar da hayaki mai dumama yanayi mai yawa, yadda kasar Sin ta dauki alhaki tsimin makamshi da rage hayaki mai gurbata muhalli ya burge shi kwarai.

Da yake magana a nan Beijing lokacin taron tattaunawar masanan kasar Sin da kasashen duniya da aka yi a nan birnin Beijing, Elkind ya ce, yanzu, kasar Sin na fuskantar wasu ayyuka da dama, ba ma kawai za ta karfafa rage talauci a kasar da raya tattalin arziki ba, hatta ma ya kamata ta nace kan tsimin makamshi da rage hayaki mai gurbata muhalli don cimma burin kamar yadda ta tsaida na yin gyare-gyare game da yin amfani da makamashi.

A karkashin wannan yanayi, furucin da Sin ta yi da matakan da ta dauka na canja salon bunkasuwarta sun dace sannan ya bayyana cewa, Sin ta gabatar da burinsa na kara yin amfani da makamashin da za a sake yin amfani da shi zuwa kashi 20 cikin 100 zuwa shekarar 2030.

Ya ce wannan ya zama wani babban buri, kuma ya nuna cewa, Sin ta fahimta alakar da ke tsakanin hayaki mai gurbata muhalli da ta fitar da ingancin iska na kasar, kuma akwai makoma mai haske wajen inganta hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka wajen yin amfani da tsabtaccen makamashi.

Mr Elkind ya ce, yanzu, Sin na canja tsarin raya tattalin arziki zuwa kara yawan sayayya, kuma Sin ta rage dogara kan raya masana'antu da habaka yin hidimomi don amfanawa kyautata tsarin amfani da makamashi da rage hayaki mai gurbata muhalli da tsimin makamashi. Haka kuma wannan mataki na canja salon raya tattalin arziki da Sin ta yi, ya zama yadda ya kamata, kuma gwamnati da masu saka jari na kasashen duniya sun yi amfani da wannan dama, don shawo kan matsalolin da take fuskanta.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China