in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzkin Afirka na fuskantar kalubale da damar samun ci gaba tare a bana
2016-01-26 12:19:34 cri

Kwararru kan harkokin tattalin arziki suna ganin cewa, a shekarar 2015 da ta wuce, matsakaicin yawan karuwar tattalin arzikin kasashen Afirka ya zarce kashi 6 cikin dari, hakan ya nuna cewa, tattalin arzikin nahiyar zai samu ci gaba cikin sauri, kuma an daukar da wasu kasashe a matsayin "sabbin kasashen da suka fi saurin samun bunkasuwar tattalin arziki" a saboda nasarorin da suka samu a fannin ci gaban tattalin arzikinsu.

A cikin shekaru goma da suka gabata, kasashen dake yankin kudu da hamadar Sahara sun samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri, amma duk da haka ci gaban tattalin arzikin nasu yana fuskantar tafiyar hawainiya, inda ya ragu zuwa matsayin da ya samu kansa a ciki a shekarar 2009.

Asusun ba da lamuni na kasa da kasa IMF ya rage hasashen da ya yi na karuwar tattalin arzikin kasashen Afirka a shekarar 2015 zuwa kashi 3.75 cikin dari, kana ya rage hasashen ci gaban da ya yi a bana wato shekarar 2016 zuwa kashi 4.25 cikin dari. Mataimakin darektan sashen kula da harkokin kasashen Afirka na asusun IMF Rodger Nolde ya bayyana cewa, hakika yawan karuwar tattalin arzikin da aka hasashe a kasashen na Afirka ya fi na wasu yankuna yawa, amma a halin da ake ciki yanzu, da kyar kasashen Afirka su samu ci gaban tattalin arzikin da aka yi zato cikin sauri.

Dalilin da ya sa kasashen Afirka suka shiga wannan hali, shi ne raguwar farashin muhimman kayayyakin, misali man fetur da ma'addinai, lamarin ya riga ya kawo cikas ga bunkasuwar tattalin arzikin wasu kasashe, misali, Najeriya da Angola wadanda ke hako man fetur, da Afirka ta kudu da Guinea da Saliyo da Zambiya wadanda ke hako ma'addinai.

Ban da haka, Rodger Nolde yana ganin cewa, akwai wani dalili na daban da ya sa kasashen Afirka suke fuskantar wahalar samun ci gaban tattalin arziki, wato rashin samu masu sha'awar zuba jari a kasashen nasu, saboda irin sharuddan ake gindayawa yayin da ake bukatar zubawa jari a kasashen Afirka.

Kazalika, gwamnatin kasar Sin tana kara kyautata tsarin tattalin arzikinta, a sanadin haka, kasar Sin ta rage yawan kayayyakin da take shiga kasar daga kasashen waje, a baya kuma, kasar Sin tana sahun gaba a cikin kasashen dake shigar da kayayyaki daga kasashen dake yankin kudu da hamadar Sahara.

Ko shakka babu, lamarin ya kawo cikas mai tsanani ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen dake fitar da kayayyakin zuwa ga kasashen waje, shi ya sa, yawan karuwar tattalin arzikin kasashe guda takwas a Afirka wadanda ke dogaro kan fitar da man fetur ya kai kashi 3.5 cikin dari kawai, amma a baya, yawan karuwar tattalin arzikinsu ya kai kashi 7 cikin dari.

A kasashen Afirka ta kudu da Ghana da Zambiya, ko da yake ba su gamu da matsala mai tsanani ba, amma su ma suna fuskantar matsin lamba a yayin da suke tsara kasafin kudinsu.

A kasashen Kwadibuwa da demokuradiyar Kongo da Habasha, duk da cewa, yawan karuwar tattalin arzikinsu ya zarce kashi 7 cikin dari, amma saboda matsalar tsaro, su ma suna fama da kalubale a fannoni da dama.

Amma Rodger Nolde yana cike da imani kan makomar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, ya ce, kasashen suna da babban karfi a asirce, duk da cewa, wasu kasashe suna da bukatar yin kwaskwarima cikin gajeren lokaci domin fuskantar kalubalen dake gabansu.

Game da kalubalen dake gaban kasashen Afirka, Rodger Nolde ya bayyana cewa, kafin watanni shida da suka gabata, asusun IMF ya gabatar da wani batun game da yawan al'umma a kasashen Afirka, an ce, ya zuwa shekarar 2035, al'ummonin kasashen Afirka za su kai rabin yawan mutanen da ke neman samun aikin yi a duk fadin duniya, ana iya cewa, wannan shi ma wata dama ce ta samun ci gaban tattalin arziki.

Ban da haka, ana fuskantar rashin daidaito a Afirka, amma idan an kyautata matsalar, ta yadda za ta dace da matsayin kasashen Asiya, tattalin arzikin kasashen Afirka zai karu a kalla kashi 1 cikin dari. Asusun IMF ya ce, ya kamata a samar da tallafin kudi ga matalauta a kasashen Afirka, ban da haka, ya kamata a rage rashin daidaici tsakanin maza da mata, hakan zai sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki a nahiyar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China