in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin Lassa ya kashe mutum daya a jihar Ikkon Nigeriya
2016-01-24 13:36:21 cri
Hukumar kiwon lafiya a jihar Ikkon Tarayyar Nigeriya ta tabbatar da mutuwar mutum daya sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa, kamar yadda kwamishinan kiwon lafiyar jihar Jide Idris ya tabbatar ma manema labarai, inda yace mamacin mai shekaru 51 yana zaune ne a yankin Ilasan Leki kuma ya rasu ne bayan da aka kai shi asibiti a makare.

Wannan mutum yana daga cikin mutane 3 da aka tabbatar sun harbo da wannan cuta a jihar.

Jide Idris yace an kuma gano wata mata mai shekaru 36 dake dauke da cutar amma a yanzu haka tana shan magani a asibitin Mainland dake birnin jihar inda ya tabbatar da cewar yanayin da take ciki yana samun ingantuwa.

Na ukun kuma inji Kwamishinan wanda a da yake a asibitin Ahmadiyya a unguwar Ojokoro shi ma yanzu yana samun jinya a babban asibitin koyarwa na jami'ar Ikko inda yake samun sauki kwarai da gaske.

Kwamishinan kiwon lafiyar na jihar Ikko ya shaida ma manema labarai cewar gwamnatin jihar ta samu sunayen mutane 447 da ake ganin yuwuwar sun kamu da cutar daga cikin su kuma ana sa ido akan 438.

A farkon wannan makon ne dai ministan kiwon lafiyar kasar ya sanar da bazuwar cutar ta Lassa zuwa jihohi 17 inda tuni ya hallaka mutane 63.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China