in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasashen yammacin Afrika shawo kan cutar Ebola
2016-01-31 10:57:43 cri

A ranar 14 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar da cewa, an shawo kan cutar Ebola da ta sake bulla a kasar Liberiya, yanzu, ana ci gaba da daukar matakai don kawo karshen cutar ta Ebola a yankunan da ke yammacin kasashen Afrika. Bayan da cutar Ebola ta addabi wadan nan yankunan a tsawo sama da shekaru 2, kasashe 3 da ke yammacin Afrika wato Liberiya, Guinea, da Saliyo sun jagoranci shirin yaki da cutar cikin nasara, kuma jama'ar yankunan wadannan kasashe suma sun shiga cikin wannan aiki, kana kasashe da dama sun ba da gudummawa yadda ya kamata, abun da ya sa aka cimma nasarar yaki da cutar. Haka kuma, jami'in hukumar ta WHO sun jinjina irin rawar da Sin ta taka cikin wannan aiki.

Bisa kididdigar da aka samu, an ce, cutar Ebola ta haddasa mutuwar mutane sama da dubu 11 da dari 3, kuma yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai sama da dubu 28 da dari 5.

Babbar magatakardan hukumar WHO Margaret Chan ta bayyana cewa, gano kwayoyin cutar Ebola da hana yaduwarsa ya zama wani babban ci gaban da aka samu, wannan ya danganta da kokarin da gwamnatocin kasashen yammacin Afrika 3 da masu aikin jinya, da kungiyoyin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, suka yi.

Yayin da kasashen da ke yammacin Afrika suke yaki da cutar Ebola, Sin ta kasance kasar data bayar da gudummawa a lokaci na farko, kuma ta tura likitoci, sannan ta ba da tallafin kudi da kayayyaki da dama don yaki da cutar.

Direktan sashen kula da bada daukin gaggawa na hukumar WHO Reeker Brennen, ya yi hira da wakilinmu, inda ya bayyana cewa, sun yaba da tallafin kayayyaki da kuma tura ma'aikatan jiyya da kwararru da dama, da kasar Sin tayi, kuma wadannan jami'ai na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen bada kulawa ga wadan da suka kamu da cutar, tare kuma da binciko mutanen da suka taba yin mu'amala da masu dauke da cutar.

A ranar 14 ga wata ne, kakakin hukumar kula da kiwon lafiya ta kasar Sin Song Shuli ya ce, game da cututtukan da ke bazuwa, kungiyar likitocin kasar Sin dake taimakawa Afrika da kwararru masu fasahar dakile yaduwar annoba da kiwon lafiya na Sin sun jajurce wajen hadin gwiwa da al'ummar kasashen Afrika tare, da yin aiki kafada da kafada don tunkarar kalubalen dake addabar kasashen. Ma'aikata masu aikin jinya sun zama tsintsiya madaurinki daya, wajen hadin gwiwa da masu horo da masu sa ido da masu aikin likitancin kasar Sin, don jagorantar aikin taimakawa kasashen Afrika wajen warware annobar, kuma sun samu jinjina daga kasashen Afrika da gamayyar kasa da kasa.

Bayan da aka shawo kan cutar Ebola, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya game da kafa tsarin kiwon lafiya don aikin sake gine-gine a kasashen yammacin Afrika, da nuna goyon baya ga hukumar WHO domin ta kafa wani asusun gaggawa, don ci gaba da bada horo ga kwararru a fannin kiwon lafiya da daidaita matsalolin kiwon lafiya cikin gaggawa.

Yayin da aka tunkari wannan annoba, akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi tunani kansu. Sakamakon tsaikon da aka samu wajen yaki da annobar, hukumar WHO ta samu kushewa da zargi daga jama'a. Margaret Chan ta ce, akwai kuskure game da matakan da hukumar WHO ta dauka wajen yaki da cutar ta Ebola, ya kamata a yi gyare-gyare game da hukumar.

Margaret ta ce, da farko dai, ya kamata a kafa tsarin cikin gaggawa, a daidaita shirye-shirye wajen kula da harkokin kasashen duniya, da daidaita matsalolin kiwon lafiya da suka kunno kai cikin gaggawa, da kafa runkunin yaki da annoba cikin gaggawa a duniya, da karfafa tsarin tattara kudade na hadin gwiwa da sauran mambobin kasashen duniya, don nuna goyon baya ga hukumar WHO da kasashen duniya dasu yaki da cututtuka, da taimakawa kasashe marasa ci gaba don yaki da annoba.

Ban da wannan kuma, a cikin wani dogon lokaci, ba a yi nazari game da cututtuka da ke bazuwa a kasashe masu zafi sosai ba, sabo da manyan masana'antu masu yin magunguna sun yi nazari bisa ga moriyar tattalin arziki kawai, abun da ya sa suka samu kushewa da dama. Amma, abun farin ciki shi ne, an yi amfani da allurar rigakafi na rVSV-ZeBOV da hukumar kula da kiwon lafiya ta Canada ta kirkiro a kasar Liberiya wato inda cututtuka ke bazuwa, hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan wannan matsala.

Bayan da aka kawo karshen aikin yaki da annobar, akwai yiwuwa cewa, wasu kwayoyin cututtuka da ke cikin jikin wadanda suka samu sauki, za su iya sake bullowa. Hukumar WHO ta ce, tsugune ba ta kare ba wajen yaki da cutar. Matakan da za a dauka don tabbatar da dakile cutar cikin sauri, da mayar da martani game da kwayoyin cututtuka wadanda za su sake dawowa, da yadda aka tabbatar da mutane masu lafiya da tsarin kiwon lafiya, sun kasance kalubalolin da kasashen yammacin Afrika guda 3 da hukumar WHO da kungiyoyin kasa da kasa da sauran kasashen duniya ke ci gaba da fuskanta yanzu.

Hakika, game da barkewar cutar Ebola, kasashen duniya sun tashi tsaye don yin nazari. Duk da irin tazarar dake tsakanin kasar Sin da kasashen na Afrika, amma hakan bai hana kasar Sin ba da nata gudummawar ba gwargwado hali.

Yayin da aka katse hanyoyin zirga-zirgar ta sararin samaniyya zuwa kasashen Liberiya, Guinea, da Saliyo da cutar Ebola tayi kamari a yammacin Afrika, kuma likitocin kasashen waje suka janye jiki daga wadannan kasashen, kasar Sin ta tura jiragen saman musamman don jigilar kayayyakin da ake bukata cikin gaggawa, kuma jami'an diplomasiyya a ofishin jadakancin Sin dake kasashen, da ma'aikata masu aikin jinya da masu aikin kiyaye zaman lafiya da injiniyoyi sun zabi ci gaba da zama a can, don yaki da annobar tare da jama'ar wadancan kasashen.

Bayan barkewar cutar ne, kasar Sin ta samar da kudaden agajin gaggawa da yawansu ya kai kudin Sin RMB miliyan 750 ga kasashen Saliyo da Lberiya, da Guinea, hakan ya sa kasar ta zama daya daga cikin kasashen da ke samar da kayayyakin agaji mafi yawa. Ban da wannan kuma, Sin ta tura masu aikin jinya da yawansu ya kai dubu 1, kana ta horar da likitoci kimanin dubu 13 na kasashen Afrika 9.

Sakamakon samun koma baya a tsarin kiwon lafiya a wasu kasashen Afrika, abun da ya kawo kalubale sosai ga hana yaduwar cututtuka a nahiyar. Kasar Sin da sauran kasashen waje sun taimakawa kasashen Afrika wajen horar da mutane da samar da fasahohi da sauran kayayyaki, abun da ya karfafa zukatan masu aikin jinya na kasashen, da basu kwarin gwiwa wajen shawo kan matsalar cutar.

Gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen yaki da annobar ta samu babban yabo daga kasashen duniya. Kakakin tawagar M.D.D. wajen yaki da cutar Ebola cikin gaggawa Fatimatou Lerena Kabba ta ce, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga kasashen yammacin Afrika wajen yaki da cutar Ebola.

Yayin da aka tabo maganar batun yaki da cutar Ebola, ya kamata a dogara kan nazari da hana yaduwa, da kirkiro da sabbin magunguna, kuma an kara kyautata wadannan ayyuka a kasar Sin da kasashen Amurka da Turai.

Bayan da aka cimma nasara wajen yin amfani da magungunan Zmapp don warkar da wadanda suka kamu da cutar, jama'a sun fara samun biyan bukatunsu na dakile cutar Ebola. A dakukuwan gwajin kwayoyin halittu na kasar Sin da kasashen Turai, bayan da aka yi gwajin aiki, an fara samun maganin da zai hana yaduwar kwayoyin cututtuka. Sa'an nan an gaggauta nazarin fasahohi da magunguna, da magungunan rigakafi, abun da ya canja yanayin da ake ciki na samun bazuwar cutar a nahiyar Afrika.

A cikin shekaru sama da 10 da suka wuce, dan Adam sun gamu da jarrabawa da dama. Bayan da aka yi yaki da cutar SARS da ta bullo ba zato, da cutar murar tsuntsaye, da cutar mura mai nau'in H1N1, kasashen duniya sun samu fasahohi da dama wajen yaki da manyan cututtuka a duniya, abun da ya aza wani harsashi wajen shawo kan cutar Ebola.

Idan har al'umma za su ci gaba da yaki da cututtuka, bayan da suka shawo kan wadannan cututtuka, za su samu ci gaba sosai. Yaduwar cutar Ebola ta sanya kasashen duniya suka ba da taimako cikin gaggawa wajen yaki da annobar. Abun da ya shaida cewa, idan kasashen duniya suka hada gwiwa tsakaninsu da ci gaba da nazari, da kafa wani tsarin sa ido, da daukar wasu muhimman matakai, hakika za a iya dakile yaduwar dukkannin cututtuka da ka iya bullowa a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China