160120-Ziyarar-shugaban-kasar-Sin-a-yankin-gabas-ta-tsakiya.m4a
|
Masu fashin baki na cewa, ziyarar za ta taimaka a kokarin da ake na shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya mai fama da tashin hankali. Bugu da kari, yankin na da matukar muhimmanci ga shirin nan na "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta bullo da shi.
Masana na ganin cewa, ziyarar da shugaba Xi ya kai wadannan kasashen uku za ta zurfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da su, kuma za ta kawo muhimmin tasiri ga yankin. A yayin ziyarar, shugaba Xi zai yi musayar ra'ayoyi da takwarorinsa na wadannan kasashe uku kan wasu muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya domin kokarin kawo zaman lafiya a yankin, har ma da duniya baki daya. Ana kuma fatan za su sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi a fannoni daban-daban.
Bugu da kari, shugaba Xi zai bayyana manufofin kasar Sin na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, tare kuma da ba da shawarwari a kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da yankin gabas ta tsakiya.
Masu sharhi na bayyana cewa, saboda tasirin siyasar Gabas ta Tsakiya ga kasashen duniya, ya zama wajibi a samar da zaman lafiya a yankin, ta yadda za a samu zaman lafiya a duniya baki daya. Masu iya magana na cewa, sai da zaman lafiya za a samu kowa ne irin ci gaba da ake bukata. (Ibrahim/Sanuisi Chen)