in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a yi amfani da fasahar yakar Ebola wajen yakar ta'addanci
2016-01-18 12:14:55 cri

A ranar 13 ga watan nan na Janairu ne aka kaiwa wani masallacin dake arewacin kasar Kamaru dake tsakiyar nahiyar Afirka harin kunar bakin wake, kana daga bisa aka dora alhakin wannan hari kan kungiyar Boko Haram. A ranar 15 ga wata, a gabashin Afirka, kungiyar Al-Shabaab ta kai hari kan wani sansanin soji na kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU, wanda ke kudancin kasar Somaliya. A dai wannan rana, an kuma kai hari ga wani otel na saukar baki dake Wagadugu, babban birnin kasar Burkina Faso, wadda ke yammacin nahiyar Afirka, jim kadan kuma wata tashar yanar gizo ta masu da'awar "jihadi" mai alaka da kungiyar al-Qaida reshen Magreb, ta sanar da cewa, ita ce ta kaddamar da harin.

Har wa yau wannan kungiya, ta taba kai hari mai kama da wannan kan wani otel na saukar baki a birnin Bamako, fadar mulkin kasar Mali, a watan Nuwambar shekarar da ta gabata. A wancan lokaci mutane sama da ashirin ciki hadda Sinawa uku sun rasa rayukan su sakamakon harin.

A halin da ake ciki yanzu, kungiyar mayaka ta Magreb dake arewacin yankin, da kungiyar Boko Haram dake yamma da tsakiyar yankin, da kuma kungiyar Al-Shabaab dake gabashin yankin, suna aikatawa laifuffukan ta'addanci a sassa daban daban a fadin Afirka, suna kuma takara tsakaninsu wajen jawo hankulan al'ummomin kasa da kasa, tare da kara yin suna a duk fadin duniya.

A nahiyar Afirka, kungiyoyin masu tsattauren ra'ayi sun fi mai da hankali ga kasashen dake cikin mawuyacin hali domin kai hare-hare, misali, kasar Burkina Faso tana cikin tsaka mai wuya, kana kasar Kamaru tana fama da karancin sojoji a arewacin yankinta, yayin da kasar Somaliya kuwa ke fama da hargitsi a ko da yaushe.

Ban da haka, tsahon lokaci, akwai sabani mai yawa tsakanin kasashen Afirka, inda da kyar suke iya hada kai domin yaki da ta'addanci, kuma yawancinsu suna fama da matsalar karancin kudade. A watan Fabrairun bara, kasashe da dama da suka hada da Najeriya, da Kamaru, da Nijar, da Chadi da Benin da sauransu sun tsai da kuduri cewa, za su kafa wata rundunar hadin kai domin yin yaki da kungiyar Boko Haram, amma ya zuwa yanzu, ba su cimma wannan buri ba saboda karancin kudi.

Kasashen Afirka suna fatan za su samu ci gaba yadda ya kamata, amma ayyukan ta'addanci sun kawo illa ga bunkasuwarsu, kuma sun lahanta imanin al'ummomin wadannan kasashe, da kuma masu zuba jari na kasashen waje. Idan dai ba a dakile yaduwar annobar ta'addanci a nahiyar ba, to kungiyoyin ta'addanci ka iya yaduwa daga Afirka, ya zuwa sauran shiyyoyin kasashen duniya baki daya.

Yayin da ake shan wahalhalu daga ayyukan ta'addanci, kasashen Afirka sun samu sakamako a fannin yaki da yaduwar annobar Ebola, har sun kai ga shawo kanta daga duk fannoni.

Hakika, annobar Ebola ta yi kama da annobar ta'addanci a wasu fannoni, misali, dukkansu biyu suna iya yaduwa cikin sauri, suna kuma iya hallaka mutane tare da haifar da fargaba mai tsanani, kana suna iya jawo hasarar tattalin arziki da gurgunta zamantakewar al'umma.

Idan an waiwayi yakin da aka yi da annobar Ebola a nahiyar Afirka, ana iya gano cewa, kusan dukkan al'ummomin kasa da kasa ne ke yin kokari tare, kuma kusan dukkan al'ummomin kasa da kasa ne ke samar da gudummuwarsu wajen samar da kwararru, da kudade da kuma fasahohin zamani. Ana iya cewa, cimma burin samun nasarar yakar annobar Ebola yana da nasaba da taimakon al'ummomin kasa da kasa baki daya. Idan an yi amfani da wannan fasaha, to ko shakka babu za a samu babban sakamako a yaki da ta'addanci, musamman ma game da bukatar taimakon MDD.

Ban da haka, abu mafi muhimmanci shi ne kasashen Afirka su kara samun bunkasuwa bisa karfin kansu, kuma kasashen duniya su kara samar da taimako gare su wajen kiyaye tsaro da kwanciyar hankali, tare da kara kyautata tsarin kiwon lafiya a nahiyar, da haka al'ummar kasashen Afirka za su kubutar da kansu daga talauci, su samu kwanciyar hankali da lafiyar jiki, har a kai ga samun nasarar dakile Ebola da ta'addanci a nahiyar baki daya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China