Kamar yadda ake samun bukukuwan gargajiya da yawa a kasashen Afirka, a nan kasar Sin ma haka yake, akwai bukukuwan da suke bayyana al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakani. A biyo mu cikin wannan shiri, inda Lubabatu tare da Maman Ada za su tattauna a kan bukukuwan gargajiya na Sinawa, da ma na kasashen Afirka.