Da yake karin haske game da lamarin, ministan ma'aikar lafiyar kasar Isaac Adewole, ya ce ya zuwa yanzu, mutane 42 ne suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar. Sai dai duk da hakan ministan lafiyar ya ja hankalin mazauna birnin na Abuja da kada su razana, su kuma dauki matakan lura, tare da kai rahoton cutar da zarar sun ga alamun ta.
Mahukuntan Najeriyar dai na cewa suna da kwarewa, da kuma ikon dakatar da yaduwar cutar ta Lassa, kuma akwai kyakkyawan hasahen samun maganin ga masu dauke da ita, muddin dai sun garzaya asibiti a kan lokaci.