160113-Takaddamar-kasashen-Saudiya-da-Iran-Sanusi.m4a
|
Mahukuntan Saudiya sun dauki wannan mataki bayan da wasu Iraniyawa masu zanga-zanga suka kona mata ofishin jakadanci da ke birnin Tehran, bayan da kasar Saudiya ta yanke hukuncin kisan kan wani Malam Shi'a da magoya bayansa bisa zargin aikata ta'addanci.
Hukumomin Saudiya sun zargi mahukuntan Iran da kasa daukar matakai domin hana kai wa ofishin jakadancinta dake Teheran da kuma karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Mashhad na Iran hare hare.
Daga bisani kuma wasu kasashe da ke bin mashabar Sunni, kamar Sudan da Bahrai, Somaliya, Djibouti da wasu kasashen Larabawa da ke marawa Saudiya baya suka sanar da yanke huldar diflomasiya da kasar ta Iran.
Masana na cewa, tun ba yau ba akwai dadaddiyar rashin jituwa ta fuskoki daban-daban tsakanin kasashen biyu, kmar batun mai, siyasar bangaranci, manufofin siyasa da neman fada a ji a yankin gabas ta tsakiya da sauran su.
Yanzu haka kuma kungiyar hada kan kasashen Larabawa wato AL a takaice, a taron da ta gudanar a kasar Masar, ta bukaci kasar Iran da ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen ba tare da bata lokaci ba, sannan suka bayyana daukar matsaya guda na nuna goyon baya ga kasar Saudiya.
Masu fashin bakin na cewa, wajibi ne kasashen biyu su kai zuciya nesa, su koma teburin sulhu don warware takaddamar da ka iya shafar daukacin kasashen duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)