160108-Kasar-Sin-ta-ci-gaba-da-yunkurin-bude-kofa-ga-kasashen-waje-a-yammacin-kasar-Lami.m4a
|
A watannin Satumba da Oktoba na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sabon shirin tattalin arziki na hanyar siliki da hanyar siliki a kan teku ta karni na 21, inda ya yi kira ga kasashen dake makwabtaka da hanyar siliki da su hada kai wajen cimma burin tabbatar da zaman wadata da kawo moriyar juna. Wannan shiri ya samu karbuwa sosai daga wajen kasashe fiye da 60 dake kan hanyar siliki, amma a sa'i daya, wasu kasashen yammacin duniya suna rashin amincewa a kansa, suna tsoron wannan shiri zai zama shirin Marshal na kasar Sin, har ma Sin za ta nemi matsayin jagoranci na wannan yanki.