in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nigeriya ya sha alwashin ganin komai ya daidaita a sabuwar shekarar nan
2016-01-02 14:11:23 cri
Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeriya ya tabbatar ma al'ummar kasar cewa gwamnatin shi a shirye take ta ga komai ya daidaita nan bada dadewa ba.

A sakon shi na murnar shiga sabuwar shekara ga al'ummar kasar ranar jumma'ar nan, ya ce yana sane cewa 'yan kasar na fuskantar wahalhalun rayuwa a cikin 'yan watannin nan, amma a cewar shi duk na dan lokaci ne saboda gwamnatin shi tana aiki tukuru na ganin 'yan Nigeriya ba tare da la'akari da matsayinsu na zamantakewa ko siyasa ba sun samu sassauci.

Shugaban yayi alkawarin cigaba da yin iyakacin kokarin shi na cika alkawarin da yayi lokacin yakin neman zabe, wanda yace ingantaccen da tabbataccen aiwatar da shirin dake kunshe cikin kasasfin kudin bana zai shawo kan batutuwa da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki da a yanzu haka suke jawo hankalin 'yan kasar.

Daga nan sai ya yaba ma rundunar sojin kasar a kan gaggarumin aikin da suka yi na dakile kungiyar 'yan ta'adda da suka addabi musamman yankin arewa maso gabashin kasar a cikin 'yan shekarun nan. Sai dai ya lura da cewa har yanzu akwai aiki mai yawa da ake bukatar yi a bangaren tsaro.

Dangane da batun cin hanci kuwa, shugaban kasar yace gwamnatin shi zata cigaba da farautar masu hannu a ciki tare da daukan matakan da ya kamata.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China