Lokacin da muke yi managa a kan musulman kasar Sin, dole a fara ambatar kabilar Hui, amma a yau, mun isa gundumar Xunhua, wadda ita ce garin kabilar Salar, wata karamar kabila ta daban dake bin addinin Musulunci a kasar Sin. Kabilar Salar na daya daga cikin kananan kabilun dake bin addinin musulunci a kasar Sin, tun daga karshen daular Yuan, 'yan kabilar Salar sun kaura zuwa nan garin Xunhua daga tsakiyar Asiya. Shi ya sa, tufafinsu na ainihi yana da siffar musamman na tsakiya Asiya, daga baya kuma, sun samu sauyawa zuwa tufafin da muka gani a yau.