160106-Halin-da-ake-ciki-a-kasar-Sham.m4a
|
A baya kasashen Rasha da Amurka da kuma kawayenta a gyefe guda sun kasa warware bambance-bambancn dake tsakaninsu game da batun kasar ta Syria, musamman ma makomar shugaba Bashar al-Assad.
Ita dai Rasha tun ba yau ba ta bayyana cewa, tana kai hare-hare a Syria ne domin yaki da 'yan ta'adda tare da kawo daidaito a halaltacciyar gwamnatin Bashar al-Assad, matakain da Rasha ta ce zai taimaka wajen samar da yanayin da ya dace ga 'yan siyasar kasar Syria ta yadda za su yi ba-ni-gishiri-in-ba-ka manda.
Da farko kasashen yammacin duniya dai karkashin jagorancin Amurka na adawa da matakan soja da Rasha ke dauka a Syria. Sannan daga bisani ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, sojojinta za su dakatar da shirinsu na horas da kungiyar 'yan adawar kasar Sham, inda za a maye gurbin shirin ta hanyar tallafa musu da makamai domin yakar mayakan kungiyar IS.
Masana a harkar tsaro na ganin cewa, da alamun an dauko hanyar warware batun kasar Syria, ganin yadda yanzu manyan kasashen da a baya kansu ke rabe suka fara fahimtar juna, duk da cewa, ba rasa wasu 'yan bambance-bambancen da ke tsakaninsu ba.
Masu fashin baki na cewa, matakin da MDD ta dauko a wannan karo da kuma abubuwa da ke faruwa a zahiri daga bangarorin da lamarain ya shafa, ana fatan haka za ta cimma ruwa, kana daga karshe za a kawo karshen yadda ake salwantar da rayukan fararen hula a kasar ta Syria. (Ibrahim/Sanusi Chen)