Kabilar Hui kabila ce mafi dogon tarihi da yawan al'umma a kananan kabilun dake zaune a lardin Qinghai na kasar Sin, kana kabila ce da ke sha'awar koyon al'adu masu kyau na sauran kabilu. Ban da wasu wurare na musamman, ba kullum ba ne 'yan kabilar su ke sanya tufafi da kayayyakin ado irin nasu, amma wannan ba yana nufin cewa,ba a ganin tufafin kabilar a dandalin tufaffin gargajiya na kananan kabilu na kasar Sin ba, a maimakon haka, 'yan kabilar na amfani da su ta wata hanya ta daban.