151225-kasar-sin-mai-launin-kore-kasar-sin-mai-kyau-142.m4a
|
A shekarar 1872, an kafa lambun shan iska na Yellow Stone a kasar Amurka, wanda ya zama lambun shan iska na farko a duniya. Bayan shekaru 143, kasashe kimanin 100 sun kafa irin wadannan wuraren shan iska fiye da dubu 6 a duniya. A ranar 21 ga watan Yuni na shekarar 2007, an bude wurin shan iska na Pudacuo na birnin Shangri-La, wanda aka kafa shi don kare naman daji da gandun daji yadda ya kamata.
Sannan kuma, a watan Satumba na shekarar bana, an kafa wurin shan iska na kiyaye naman daji na farko na kasar Sin wato wurin shan iska na gwankin Tibet da shanun daji mai suna "Qiangtang" a birnin Lhasa, wanda fadinsa ya kai Square kilomita dubu 298, aka kira shi "gida mafi kyau na naman daji".