in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma Li, 'yan kabilar Hui, wadda ta kirkiro wani nau'in tufafin gargajiyar kabilarsu, ta hanyar amfani da salon gargajiya da na zamani
2015-12-28 15:48:46 cri

 


 


Kabilar Hui kabila ce mafi dogon tarihi da yawan al'umma a kananan kabilun dake zaune a lardin Qinghai na kasar Sin, kana kabila ce da ke sha'awar koyon al'adu masu kyau na sauran kabilu. Ban da wasu wurare na musamman, ba kullum ba ne 'yan kabilar su ke sanya tufafi da kayayyakin ado irin nasu, amma wannan ba yana nufin cewa,ba a ganin tufafin kabilar a dandalin tufaffin gargajiya na kananan kabilu na kasar Sin ba, a maimakon haka, 'yan kabilar na amfani da su ta wata hanya ta daban. Kwanan baya, abokiyar aikinmu Tasallah ta yi tattaki zuwa birnin Xining na lardin Qinghai dake yammacin kasar Sin, inda ta ziyarci wata yarinya 'yan kabilar Hui, wadda ta kirkiro wani nau'in tufafin gargajiyar kabilarsu, ta hanyar amfani da salon gargajiya da na zamani.

A lokacin da rana ke daf da faduwa, ana iya ganin musulmai maza a titunan dake birnin Xining na lardin Qinghai, sanya hula mai launin fari irin ta kabilar Hui suna tafiya babban masallaci na Dong Guan, don yin sallah. kana yawancin kantunan dake dab da masallacin suna sukan rufe domin zuwa sallah, amma kantin "Noor" a bude ya ke, inda mutane da yawa ke sayen tuffafi da kayayyakin ado.

Malama Ma Li ita ce mai wannan kantin, kuma tana tarbar masu sayen kayayyaki da hannu bibbiyu. A watan Mayu na shekarar 2015, wannan yariniya 'yar kabilar Hui ta bude kantinta na farko dake tsara da sayar da tufaffi da kayayyakin ado samfurin Noor ga musulmai mata. Bayan rabin shekara kawai, a yanzu haka ta bude kantuna guda biyu, kuma dukkansu na samun ciniki sosai.

Ma Li ta ce, bayan da ta kammala karatu a jami'ar nazarin harkokin kudi ta lardin Yunnan,sai ta komo garinsu, amma abin da ya ke damunta kullum shi ne, yadda za ta sayi tufaffi na zamani, wadanda su ka dace da tsarin Musulunci. Kamar yadda sauran 'yan mata musulmai suke yi, ita ma idan ta sayi tufaffi na zamani sai ta baiwa tela, doya gyara su ta yadda tufaffin za su dace da tsarin tufafi na musulmai. Amma, wannan hanya tana daukar dogon lokaci, saboda haka, sai tunanin bude kantin tufaffi da kayayyakin ado ya zo mata.

"Ni musulma ce, amma ina fuskantar matsala wajen sayen tufafin da suka dace da addinin musulunci. Wasu 'yan mata saboda basa bin tsarin addini musulunci, shi ya sa suke sayen kayayyakin da ke nuna tsiraici, kuma hakan ya sa sannu a hankali za a yi watsi da al'adun kabilarmu. Na yi tunanin cewa, ko zan iya yin wasu abubuwa ga 'yan uwanmu musulmai 'yan kabilar Hui? Ko zan iya samar musu tuffafin da ba sai tela ya sake gyarawa idan an saya ba? Ta yadda 'yan uwanmu mata musulmai za su iya sanya tufaffin musulmi dake hade da salon gargajiya da na zamani."

Ko da yake wannan ra'ayin Ma Li ne, amma zai yi matukar wahala wannan ra'ayi nata ya tabbata. Ma Li ta koyi fasahar sarrafa kudi a jami'a, ba ta san kome ba game da tsara tufaffi ta tafiyar kanti. Ban da wannan kuma, a lokacin tana aiki mai kyau a wani babban kamfani, sannan ta yi aure har ta haifu. Sannu a hankali ta kusan mantawa da wannan tunani ko ra'ayi, sai wata rana ta gamu da wani mai tsara tufaffi a lokacin da ta je yawon shakatawa a kasashen waje,.

"Mun fara mu'amula ne a bayan da na ba ta kyautar wani jan baki. A lokacin hankali na ba ya wajen ta, koda ya ke na dan taba ta, shi ne muka kalli juna, sai na mika mata jan bakin ,wannan ya burge ta sosai. Tun daga lokacin ne, sai muka kulla abota. A hirar da muka yi ta yara gizo, na fahimci cewa, tana sayar da tufaffi, kana mai tsara tufaffi ce, kuma ta samu nasara a wannan harka. Tana cinikayya da 'yan kasashen ketare, ta kan fitar da kayayyakinta zuwa kasashen Masar, Saudiya da dai sauransu. A ganinta ma tunani na ya yi daidai da nata, ta ce ba ta taba gamu wa da wani mutum da yake da ra'ayi da ya burge kamar wannan ba. Ta gaya min cewa, tana son ta taimake ni da dabaru ko fasahohin tsara tufaffin da nake bukata."

Bayan ta sanar da iyayenta da 'yayanta ra'ayinta na bude kantin tufaffi, sai suka nuna rashin amincewarsu da wannan shawara, amma mijinta da iyayen mijinta sun yi na'am, sun kuma nuna mata kwarin gwiwa sosai. Mahaifin mijinta ya ce,

"Tana da kwarewa a fannin, tana da basira. Tun ba yau ba ta ke wannan tunani, don haka kamata ya yi mu goyi baynta. Yariniya mai kirki, saboda haka babu wata matsala. Dukkan kayayyakin musulmai da ta ke sayarwa babu jabu, ina da tabbas a kai. Ina goyon bayan ta sosai. Lallai tana da makoma mai kyau."

Sakamakon irin goyon baya da ta samu, Ma Li ta soma sana'arta.inda suka fito da kayayyaki sanfurin Noor sakamakon kokarin da ta yi tare da abokiyarta mai tsara tufaffi,.

An tsara tare da fito da tufaffi a karon farko, kuma nan da nan aka sayar da su. Ma Li ta yi farin ciki kwarai da wannan nasara, sai dai kashi na biyu na kayayyakin da suka fitar ba su samu karbuwa ba kamar na karon farko. Game da wannan, Ma Li ba ta yi bakin ciki ba, a maimakon haka ta yi nazari sosai kan dalilai da suka haddasa rashin karbuwar kayan.

"Tsarin tufafin bai dace ba, mutane da yawa ba su son su, lallai wadannan tufaffin tsarin zamani ya yi musu yawa. Daga baya sai na soma yin bincike game da yanayin kasuwa. Inda na gayyaci tsoffi mata da su sanya tufaffin da suke jin a ra'ayinsu yana kyau, sannan na kan kalli tuffafin da wasu mutane suka sanya. Sannu a hankali, na gano wane irin tufaffi ne da za su fi samun karbuwa a cikin al'umma. A da, na tsara tufaffi ne bisa ra'ayi na, daga bisani na fahimci cewa, wannan ba daidai ba ne."

Bayan da ta shafe tsawon wata guda tana gudanar da bincike Ma Li ta fahimci cewa, tufaffi da kayayyakin ado na iya nuna hayayya da tunanin wata kabila. Saboda haka, idan ana bukatar bunkasuwar tufaffi da kayayyakin ado na wata kabila dole ne ayi la'akari da batun addini da al'adun gargajiyar kowa ce kabilar da dai sauransu.

Daga bisa ni sai Ma Li da abokiyar aikinta suka soma shigar da salon zamani kadan a yayin da suke tsara tufaffin gargajiyar kabilar Hui ta hanyar zana layi, tare da hada wasu kayayyakin ado na saka a cikin launukan kayayyakin gargajiyar kabilar wato baki da ruwan toka.

Ba shakka, sabbin tufaffi da suka tsara sun samu karbuwa sosai. Cinikayyar Ma Li tana ta samu ci gaba, har ma ta kulla abokantaka da wasu abokan cinikayyarta

Daya daga cikinsu ita ce, Han Yuru 'yar shekaru 22 a duniya.

"A da, na kan sayi tufaffi a manyan kantuna, daga baya sai na nemi tela don ya sake gyarawa. Wata rana na gano wannan kanti,kuma tufaffin da suke sayarwa suna da kyau, ina son su sosai, kuma sun dace da musulmai, sun kuma dace da zamani. Na sayi tufaffi da 'yan kwali da yawa a nan, maigida na ya ce, yanzu na iya ado. Da kyar a samu kamar wannan kanti, tuffafin da suke sayarwa sun dace da 'yan mata musulmai, su ne irin kayan da mu 'yan mata muke so."

Ba 'yan mata kawai ba ke sha'awar samfurin Noor, har da tsoffi mata da masu kiba su ma su kan sayi tufaffi a kantin na Ma Li, saboda Ma Li ta kan tsara tufaffin da za su dace da su,kuma cikin araha.

Saboda ci gaban da Ma Li ta samu, samfurin kayanta na Noor yana ta shahara a tsakanin musulmai dake birnin. Saboda haka, iyayenta su ma kara goyon bayan ta. Mahaifiyarta Ma Shuying ita ma ta kan sanya tufaffin da ta tsara.

"Idan mata sun shiga harkar kasuwanci, ko shakka babu ba su da isashen lokacin kula da iyali. Saboda haka, da farko ni da mahaifinta da yayarta mun yi adawa da wannan. Amma, yanzu mun gano cewa, tana samun ci gaba a sana'ar da ta ke yi, don haka,mu ka kwantar da hankalinmu, muka kuma amince da abin da ta ke yi. Yanzu har na kan sanya tufaffin da ta ke sayarwa."

Ma Li ta gaya mana cewa, dalilin da ya sa ta kafa samfurin Noor, shi ne sanya dukkan musulmai mata, ciki har da mahaifiyarta su kara kyan gani, da kara yin imani da kansu, ba tare da sun saba dokokin addinin musulunci ba.

"Iyaye na masu bin addinin musulunci ne. Wannan ya sa na kafa wannan samfuri domin yada al'adun gargajiyar kabilarmu. Kamata ya yi mu samu ci gaba, amma wannan ba ya nufin cewa, mu yi watsi da al'adunmu na gargajiya. Na taba karanta wata jimla 'the beauty of the woman comes from the noor of Allah', wato kyawun mace daga Allah ne. Ina fatan samfurin Noor da na kafa zai taimaka wajen samar da haske kamar yadda sunan ya nuna, har ma zai iya taimake ni wajen cimma burina na kiyaye al'adun gargajiya da tsarin suturar musulunci.

Yanzu, samfurin Noor ya shahara sosai a wasu larduna da dama da musulmai ke zama. Wata rana, wani dan kasuwa daga kasar Malaysia ya tattauna da ita, yana mai fatan shigar da tufaffin da ta tsara a kasuwar kasarsa.  

"A yayin da na yi tunani game da sunan samfurin tufaffi na, na yi la'akari da bunkasa sana'ar a kasashen ketare wata rana. Wata abokiya ta ta taba tambaya na cewa, ki ka sanya sunan samfurin kayanki da Turanci, za a iya gane wa? Na amsa mata cewa, ba a cikin kasar Sin kawai ba na ke sayar da tufaffina, mai yiwuwa ne a nan gaba zan sayar da su a ketare, sunan Turancin da na saka zai taimaka wa masu sayen kayayyaki na ketare fahimtar samfurin. Na yi imanin cewa, idan kana da buri, to wata rana hakar ka za ta cimma ruwa." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China