Abudullahi Ibrahim Mahuta, dan majalisar dokokin jihar Katsina ta Nijeriya da ya zo kasar Sin don halartar taron kara-wa-juna-sani na M.D.D. da kasar Sin ta shirya, yayin da ya zantawa da wakilinmu Bako, ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a dandalin duniya, musamman a nahiyar Afrika, kuma ya ce, kofofin Nijeriya a bude ga kasar Sin, ganin manyan kamfanonin kasar Sin da dama suna gudanar da harkoki a Nijeriya, yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da hadin gwiwa a tsakaninsu.(Bako)
151223-ya-kamata-kasashen-Sin-da-Nijeriya-bako.m4a
|