A cikin jawabin da ya yi ma al'ummar kasar a Kigali babban birnin kasar, Shugaba Kagame ya yi watsi da kudurin kasashen yammaci na gurgunta sakamakon zaben raba gardamar a kan kundin tsarin mulkin kasar. Sakamakon zaben na ranar jumma'a ya nuna cewar kashi 98% sun jefa amincewar su.
Amurka ta bayyana rashin jin dadin ta cewar an shirya zaben raba gardamar a cikin kankanin lokacin don yin gyara a kundin tsarin mulkin kasar da kuma cire tsawon wa'adin shugaban kasar a ciki.
A cikin sanarwar da fadar white house ta fitar ranar asabar, ta ce bayan yaba ma al'ummar kasar Rwanda na aiwatar da 'yancin su lami lafiya , Amurka ba ta ji dadin yadda zaben bai ba da wadataccen lokaci da dama ga muhawaran siyasa ba a kan alfanu ko rashin alfanun abin da ake niyyar yi.
Tawagar kungiyar tarayyar Turai a Rwandan ita ma ta bayyana damuwar ta cewa mako daya da aka shirya aiwatar da zaben raba gardamar kasar ba ta yi bayani sosai akan sauyin da za'a yi a cikin kundin tsarin mulkin ba balle ta samar da lokacin isashe da dama na yin muhawara.(Fatimah Jibril)