in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan kayayyakin more rayuwa da aka gina a Afirka bisa taimakon Sin
2015-12-15 14:49:15 cri

Kasar Sin ta fara taimaka wa kasashen Afirka wajen samar da kayayyakin more rayuwa ne a tun shekarun 1950, domin kyautata ayyukan raya tattalin arizki a nahiyar. Zuwa yanzu, manyan kayayyakin da aka samar a nahiyar Afirka bisa taimakon kasar Sin sun kasance wata alamar zumunci dake tsakanin Sin da Afirka, wadanda kuma suke samun yabo daga wajen mazauna yankunan. Kayayyakin sun hada da layin dogon da ya hada Tanzania da Zambia, tashar jirgin ruwa ta Zumunci dake Mauritania da kuma cibiyar taron kungiyar AU dake Addis Ababa, da dai sauransu.

Ga kuma rahoton da malam Ahmad ya hada mana dangane da wannan batu:

Layin dogon da ya hada Tanzania da Zambia, wanda aka gina bisa rancen kudi da babu ruwa cikin sa, wanda gwamnatin kasar Sin ta samar, ya kasance aiki mafi girma da Sin ta ba da taimako wajen ginawa a Afirka. Layin dogon ya fara ne daga babban binin kasar Tanzania, Dar es Salaam a gabashi, yayin da ya kare a birnin Kapiri Mposhi na kasar Zambia a yammaci, baki daya ya kai tsawon kilomita 1860.5, yayin da kilomita 977.2 na cikin kasar Tanzania ne, sai kuma kilomita 883.3 a cikin kasar Zambia. An fara aikin gina layin dogon ne a watan Oktoba na shekarar 1970, wanda ya kammala a watan Oktoba na shekarar 1975, sa'an nan kuma, a watan Yuli na shekarar 1976, an mika layin dogon ga gwamnatocin Tanzania da Zambia a hukumance.

Layin dogon da aka shimfida tsakanin Tanzania da Zambia ya kafa wata sabuwar hanya ga wasu kasashen na Afrika wadanda basu da mafitar teku, ya kuma taimakawa jama'ar kudancin Afirka wajen samun 'yancin kansu, sannan ya ba da babbar gudummawa ga kasashen dake kewayen layin dogon wajen raya tattalin arzikin su. A bangare guda, layin dogon Tanzania-Zambia ya kasance alama ta kyakkyawan zumunci dake tsakanin al'ummomin Sin da Tanzania da Zambiya, har ma da al'ummomin kasashen Afirka baki daya.

Kazalika, a lokacin da aka gina layin dogon Tanzania-Zambia, ba kawai gwamnatin kasar Sin ta samar da taimakon rancen kudi ba tare da karbar kudin ruwa ba ne, har ma ta aike da masana da injiniyoyi sama da dubu 50 zuwa inda ake aikin gina layin, haka kuma, bayan da aka mika layin dogo ga gwamnatocin Tanzania da Zambia, kasar Sin ta ci gaba da samar da taimakon kudade domin gyara da kuma kiyaye layin din.

Idan kuma aka yi tsokaci kan tashar jirgin ruwa ta Zumunci dake kasar Mauritania, wadda aka shafe shekaru 15 wajen ginawa, bisa taimakon gwamnatin kasar Sin a shekarun 1970, wannan aiki ya ba da babban tasiri ga kasar Mauritania, an kuma bayyana ta a matsayin alamar 'yancin kai na kasar.

Kafin shekarar 1963, babu tashar jirgin ruwa a babban birnin kasar Mauritania, Nouakchott, shi ya sa a shekarar 1971, gwamnatin kasar Sin ta aike da wata tawagar masana zuwa kasar domin yin bincike, sa'an nan kuma, an fara aikin gina tashar a watan Afrilu na shekarar 1979 a hukunce, yayin da aka kammala aikin a karshen watan Yuli na shekarar 1986, haka kuma, gwamnatin kasar Sin ta mika ikon tashar ga gwamnatin Mauritania a watan Oktoba na wannan shekara a hukunce, wadda ta fara aiki a shekarar 1987.

Tashar jirgin ruwa ta Zumunci na fuskar tekun Atlantic, tana kuma fuskantar mugun yanayi wanda ya kan lalata kayayyakin ginin tashar jirgin ruwa, lamarin da ya haifar wa ayyukan yin bincike a wurin da na gina tashar da matsaloli da dama. A lokacin da aka gina tashar, a kan warware matsalolin da ake gamuwa da su ta hanyar kokarin hadin gwiwa a tsakanin masana Sinawa na fannoni daban daban da injiyoyin gina tashar da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa kasar Mauritania, wadanda suka yi ta bincike, da tsarawa da kuma aiwatar da ayyukansu cikin himma da kwazo, lamarin da ya sa, aka cimma nasarar gudanar da aikin daga karshe.

Tashar jirgin ruwa ta Zumunci ta ba da babbar gudummawa wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Mauritania, inda ake shigar da hajoji kashi 90 bisa dari da wannan kasa take bukata, haka kuma, a halin yanzu, ta kasance babbar tashar jirgin ruwa ta yammacin kasashen Afirka baki daya.

Dangane da cibiyar taron kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU kuwa, ta kasance daya daga cikin manyan matakai 8 da gwamnatin kasar Sin ta fidda a yayin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato (FOCAC) da aka gudanar a binin Beijing a shekarar 2006, domin ciyar da dangantakar dake tsaknin Sin da Afirka gaba. Wannan shi ne aiki mafi girma da kasar Sin ta ba da taimako wajen ginawa a Afirka bayan layin dogon Tanzania-Zambia, wanda ya karfafa zumuncin mai tarihi dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi.

Cibiyar taron AU tana birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wanda ya kasance cibiyar siyasa da tattalin arziki na kasar, gami da babbar cibiyar da ake gudanar da harkokin diflomasiyyar nahiyar Afirka, inda akwai ofisoshin jakadanci da hukumomin kasa da kasa sama da 120, ciki har da hedkwatar kungiya ta AU. Gaba daya fadin cibiyar ya kai muraba'in mita 51,877, haka kuma aka gina cibiyar bisa taken "yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka domin ci gaban nahiyar Afirka baki daya". Wannan cibiyar ita ce daya daga cikin gine-gine mafi girma, kuma na zamani da kasar Sin ta ba da taimako wajen ginawa a Afirka, wadda aka fara aikin ginawa a watan Yuni na shekarar 2009, yayin da aka kammala aikin a watan Disamba na shekarar 2011. Kaza lika, an gudanar da bikin kammala aikin gina cibiyar a yayin taron shugabannin kungiyar AU karo na 18 a watan Janairu na shekarar 2012. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China