in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake bullo da matakan hadin gwiwa da nahiyar Afirka
2015-12-10 15:51:14 cri

A ranar Asabar 5 ga watan Disamban shekarar 2015 ne aka kammala taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, taron kolin dandalin na farko da aka gudanar a nahiyar Afirka.

A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wasu matakan hadin gwiwa 10 da nahiyar ta Afrika wadanda ake fatan aiwatarwa cikin shekaru 3 masu zuwa don ingiza dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Masu fashin baki na cewa, wannan mataki yana kara kawar da mummunar fahimtar da kasashen yamma ke yiwa dangantakar da ke tsakanin sassan biyu.

Wadannan fannoni da za a mayar da hankali a kan su sun hada da masana'antu, aikin gona na zamani, manyan ababen more rayuwa, hada-hadar kudi, raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Haka kuma akwai bangaren ciniki da zuba jari, kawar da talauci da amfanawa jama'a, kiwon lafiya, al'adu da kuma shimfida zaman lafiya da tabbatar da tsaro.

Don ganin wannan shiri ya tabbata, Sin ta yanke shawarar samar da kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 60, wannan ya kunshi bashin da babu ruwa a cikinsa na dalar Amurka biliyan 5, da kudin rance masu gatanci da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 35, kuma Sin za ta kebe dalar Amurka biliyan 5 ga asusun raya kasar Sin da kasashen Afrika da dala biliyan 5 na daban ga aikin raya kananan da matsakaitan masana'antu, kuma Sin za ta kafa asusun raya hadin gwiwar masana'antu tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, inda za a kebe masa dalar Amurka biliyan 10.

Masana na cewa, yanzu dai zabi ya rage ga kasashen na Afirka da Sin ta tanadi wannan garabasa domin su don ganin sun ci gajiyar wannan dama. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China