A yau Jumma'a hudu ga wata ne aka bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, inda shugabanni da kusoshin kasashen Sin da Afirka suka zauna tare domin tattauna harkokin hadin gwiwa a tsakaninsu ta fannoni daban daban. Shekarar bana ita ce ta cika shekaru 15 da aka kaddamar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, kuma taron kolin da aka gudanar a wannan karo ya kasance na farko da aka gudanar a nahiyar Afirka, don haka, taron na da muhimmanci sosai, da kuma ma'ana ga ci gaban huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka.
A biyo mu cikin shirin, domin samun karin haske a kan taron.(Lubabatu)
151204-Sin-da-Afirka-mu-rike-hannun-juna-lubabatu.m4a
|