Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 15 wajen kafuwar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka(FOCAC), kuma za a kira taron koli na dandalin a kasar Afirka ta Kudu a watan Disamba mai zuwa.
Tun bayan da aka kaddamar da taron, mu'amalar al'ummomi da al'adu dake tsakanin Sin da Afirka na ta samun ci gaba, kuma ana ta samun karin dalibai Hausawa da suke zuwa kasar Sin domin yin karatu a jami'a. Don haka muka samu wassu hotunan da muka dauka dangane da zaman rayuwar wassu dalibai Hausawa na jami'ar fasaha da koyarwa ta Tianjin watau TUTE na kasar Sin.
Muhammad Salim Garba, dan jihar Kano ke nan, yana wasa a cikin jami'a bayan babbar kankara da aka yi. Salim ya yi shekaru biyu yana karatu a jami'ar TUTE dake birnin Tianjin na kasar Sin, domin neman digiri na biyu a fannin injiniya a fannin na'urori ko kayayyakin laturoni.
Kabiru Abbati Dankanti na karatu cikin aji. Kabir na neman digirinsa na farko a jami'ar TUTE, kuma wannan ita ce shekara ta biyu da ya fara karatu a nan kasar Sin.
Malam na koyar da dalibai yadda ake bincike na'urori cikin ajin gwaji.
Ana nuna al'adun shayi na kasar Sin cikin ajin al'adun gargajiyar Sin. Ana shirya wassu darussa game da al'adun kasar Sin domin kara fahimtar da daliban ketare kan harkokin kasar Sin, da kuma karfafa mu'amalar dake tsakanin Sin da kasashen ketare.
Salim na wasan kallon kafa a filin wasa na jimi'ar sa.
Abokan Sinawa na koyar wa Adamu Mohammed Jajere wasan gudu da takalmi mai taya. Jajere wanda ya zo daga arewacin Nijeriya ya na karatu a sashen injiniya a fannin na'urori ko kayayyakin lantarki na jimi'ar TUTE kimani shekara daya da watanni biyu.
Ga kuma abokammu na masu wasan gudu kan takalman taya.
Ana yawon shakatawa a titin al'adun gargajiya dake birnin Tianjin. An yi zanen jirgin ruwa dake hannun Jajere da sukari mai launin ja, wani irin fasahar gargajiya ta kasar Sin.
Dalibai Hausawa dake jami'o'i daban daban a birnin Tianjin su kan yi shagali tare, huldar dake tsakaninsu na tafiya dai-dai cikin mutunci da aminci.