in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da Afrika zai bude sabon shafin hadin gwiwa a tsakaninsu
2015-12-04 13:30:13 cri

A jiya Alhamis ne aka kaddamar da taron masu masana'antun Sin da Afrika karo na 5, inda aka gudanar da shawarwari tsakanin shugabanni da wakilan 'yan kasuwa, da masu masana'antu na kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu.

Taron wanda aka yiwa lakabi da "hadin gwiwar moriyar juna da samun bunkasuwa tare", ya shafi sha'anin shigar da hanyoyin samar da kayayyaki zuwa sassan duniya na kasar Sin, da yunkurin raya masana'antu a kasashen Afrika, wadanda suka jawo hankalin masu ruwa da tsaki matuka.

A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin da kasashen Afrika sun karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannin samar da kayayyaki yadda ya kamata, karkashin hakan bangarorin biyu sun inganta hadin gwiwa a fannonin sifirin jiragen kasa, da wutar lantarki, da sarrafa sinadarai, da kirkire-kirkire, da kuma fannin sadarwa.

A sa'i daya kuma, gine-ginen da Sin ta gudanar na kunshe da fasahohi na zamani, kuma ingancinsu da saurin kammalar su ya kai ga matsayin koli. Manyan ayyuka kamar hanyoyin jiragen kasa da ke kewayen tekun Nijeriya, da hanyoyin jiragen kasa da ke hada Mombasa da Nairobi a Kenya, sun jawo hankalin jama'a sosai. Kaza lika yankunan masana'antu da Sin ta gina a nahiyar Afirka, yawancin su ke da alaka kwarai da sha'anin hadin kai a fannin kera kayayyaki. Jimillar kudin da aka zuba jari a nahiyar ya kai dalar Amurka biliyan 4.68. Don haka ana iya cewa yadda kasar Sin da kasashen Afrika ke hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki na da matukar armashi, kuma akwai makoma mai haske game da wannan fanni.

Game da hakan, mataimakin ministan kula da masana'antu da sadarwa na Sin Liu Lihua ya ce,"A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta samu ci gaba mai ma'ana, kuma tana da fasahohi da dama. A sa'i daya kuma, dangantakar da ke tsakanin ta da kasashen Afrika ta samu bunkasuwa sosai. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, ya kamata a yi hadin gwiwar da zai haifar da cimma moriyar juna, kuma akwai makoma mai haske a fannin sha'anin masana'antu da tattalin arziki, da harkokin sadarwa."

Game da bangaren Afrika ma, kasashen Afrika na yunkurin raya masana'antu a kasashensu, kuma zamanintar da sana'o'i a kasar Sin ya kawo kwarin gwiwa ga kasashen Afrika. Don game da hakan, mataimakin minista mai kula da cinikayya da masana'antu na Afrika ta Kudu, Mzwandile Masina ya ce, "Mun sani cewa kasashen Afrika ba su da muhimman ababen more rayuwa sosai, shi ya sa muke fata za a inganta yunkurin raya masana'antu, da muhimman ababen more rayuwa a nahiyar. Ban da wannan kuma, muna bukatar hadin gwiwa, don yakar talauci, da karancin guraben aikin yi, da rashin samun daidaito dake addabar mu tsahon lokaci. Hakika kasar Sin ta samar da kwarin gwiwa ga nahiyar mu a wannan fanni."

A sa'i daya kuma, bayan da tattalin arzikin Sin ya samu saurin bunkasuwa tsawon lokaci, kuma kasar Sin tana da kwarewa a fannin hadin gwiwa da kasashen Afrika, da kuma biyan bukatunsu a wasu sana'o'i da masana'antu, shugaban kwamitin sa kaimi ga yin cinikayyar kasa da kasa na kasar Sin Jiang Zengwei ya ce, "Bayan kyautata salon raya tattalin arzikin Sin, da raya kasa cikin 'yan shekarun nan, yanzu, akwai babbar dama ta inganta hadin gwiwar kasar Sin da kasashen duniya wajen samar da kayayyaki, musamman ma game da ingancin kayayyaki. Ana iya tabbatar da nagartar kayayyakin da Sin ta kera, kuma suna da araha. Yayin da kasashen Afrika ke samun bunkasuwa, akwai babbar kasuwa a nahiyar, lamarin da ya haifar da wani babban dandalin hadin gwiwar bangarorin biyu."

Sai dai abun da ya kamata a yi la'akari da shi a nan shi ne, yayin da kasar Sin da kasashen Afrika ke gudanar da hadin gwiwa game da masana'antu, ba ya ga sayar da kayayyakin da masana'antunta suka samar wadanda suka wuce kima ga nahiyar Afrika, a sa'i daya kuma kasar Sin na dora muhimmanci kwarai ga ingancin kayayyakin, da kyautata kwarewar kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa da kansu. Game da wannan fanni, shugaban kamfanin kera kayayyakin gine-ginen kasar Sin Song Zhiping ya ce, "Muna nuna goyon baya game da bunkasuwar nahiyar Afrika, mun samar musu kayayyaki masu kyau, mun kawo kyawawan fasahohi da nau'rori ga kasashen Afrika, kuma a yanzu baya ga kera nau'rori, muna kuma saka jari a nahiyar Afrika. Dalilin da ya sa, muka shiga cikin Afrika, baya ga gudanar da hadin gwiwar masana'antu a fannin samar da kayayyaki, muna kuma taimakawa kasashen nahiyar wajen kafa tsarin masana'antu na kan su."

Ko shakka babu, hadin gwiwa a fannin samar da kayayyyaki zai bude wani sabon babi, na hadin gwiwa da moriyar juna a tsakanin sassan biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China