in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma
2015-12-03 15:03:22 cri

A jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma a birnin Pretoria, inda shugabannin biyu suke ganin cewa, huldar dake tsakanin Sin da Afrika ta Kudu na cikin zarafi mai kyau, don haka bangarorin biyu za su ciyar da huldarsu gaba ta hanyar aiwatar da matsaya daya da suka cimma bisa tsarin hadin gwiwa dake tsakanin su nan da shekaru 5 zuwa 10, tare da yin amfani da taron Johannesburg na dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC.

Kafin shawarwarin, Shugaba Xi da Uwargidansa Peng Liyuan sun samu tarba ta alfarma lokacin da suka sauka a kasar ta Afrika ta Kudu. Sannan daga bisani, Shugaba Jacob Zuma ya jagoranci bikin maraba da shugaba Xi a harabar da ke fadarsa ta Union Buildings, inda aka harba bindiga sau 21, daga nan sai shugabannin biyu suka duba faretin ban girma tare.

A yayin shawarwarin, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Afrika ta Kudu dukkansu sun dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakaninsu. Dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu ta rika samun bunkasuwa mai kyau, bangarorin biyu sun kara imani da juna, hadin gwiwarsu a fannoni daban daban ta gudana yadda ya kamata, hakan ya kawo moriya sosai ga jama'arsu. Xi ya kara da cewa,

"Mun tsai da kudurin sa kaimi ga hadin gwiwar Sin da Afirka ta Kudu bisa manyan tsare-tsare da hangen nesa, baya ga nuna goyon baya ga juna kan harkokin dake da nasaba da babbar moriyar juna. Ban da haka kuma, kasashenmu biyu za su hanzarta aiwatar da 'tsarin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu nan da shekaru 5 zuwa 10', a kokarin samun kyawawan sakamako cikin ayyukan hadin gwiwarsu a fannonin raya yankunan musamman na tattalin arziki, tattalin arzikin teku, masana'antu, makamashi, manyan ababen more rayuwa, da kuma albarkatun kwadago, ta yadda zai amfani jama'ar kasashen biyu."

Bugu da kari, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana son hada kai tare da Afrika ta Kudu wajen yin hadin gwiwa a fannonin masana'antu da makamashi, ta yadda hukumomin hada-hadar kudi na Sin za su kara zuba jari a Afrika ta Kudu domin kara yin hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudi, da gaggauta kafa reshen Afrika na sabon bankin neman samun bunkasuwa na kasashen BRICS, ta yadda zai taimakawa kasar Afrika ta Kudu da sauran kasashen Afrika.

A wannan rana, kasashen biyu sun daddale yarjeniyoyin hadin kimanin 23, wadanda suka shafi tattalin arziki da cinikayya, al'adu, kimiyya da fasaha. Game da wannan, Shugaba Jacob Zuma ya ce, Kasar Afrika ta kudu tana fatan bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kimiyya da fasaha da makamashi da kayayyakin teku da zirga-zirgar jiragen sama da kuma harkokin tattara kudi, kana tana maraba ga kamfannonin Sin da su zuba jari a kasar.

A gobe ne shugabannin kasashen biyu za su jagoranci taron koli na dandalin FOCAC da za a bude a birnin Johannesburg. Shugaba Xi ya furta cewa, a yayin taron, Sin da Afirka za su bullo da matakan hadin kai a tsakaninsu nan da shekaru uku masu zuwa, baya ga kara azama ga yunkurin raya masana'antu da ayyukan gona na zamani na Afirka, a kokarin taimaka wa Afirka wajen samun dauwamammen ci gaba bisa karfin kanta. Xi yana mai cewa,

"Ni da shugaba Zuma muna saran tattauna batutuwan sada zumunta, da manufofin samun bunkasuwa tare da shugabannin kasashe daban daban, ta yadda za mu bullo da sabbin matakan da za su karfafa kyakkyawar makomar hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a nan gaba. Na yi imanin cewa, taron kolin zai zama wani gaggarumin taro da zai kara karfafa hadin kai tsakanin bangarorin biyu, wanda ba shakka zai bude wani sabon babin inganta hadin kai irin na samun moriyar juna da neman ci gaba tare ga bangarorin biyu".(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China