151127-Hakikanin-hali-na-janye-jarin-kasashen-waje-daga-kasar-Sin-Lami.m4a
|
Kwanan baya, an ba da rahoton zuba jari na duniya a gun taron cinikayya da bunkasuwa na MDD cewa, a sakamakon lalacewar halin ciniki da tashe-tashen hankali a fannin siyasa a wasu shiyyoyi, yawan jarin da aka zuba a kasashen waje a shekarar 2014 a duk fadin duniya ya kai dalar Amurka biliyan 1230, wanda ya ragu da kashi 16 cikin dari. Amma a bangaren kasar Sin, ta jawo jarin kasashen waje da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 129, wadda ya fi na kasar Amurka yawa, ta haka ta zama kasa da ta fi jawo jarin kasashen waje a duniya.