151030-Aikin-tallafawa-matalauta-ya-gudana-yadda-ya-kamata-a-kasar-Sin-Lami.m4a
|
A ranar 17 ga watan Oktoba wato ranar Asabar ta makon da ya gabata ita ce ranar kawar da talauci ta duniya. MDD ta tsai da wannan rana ce a gun taron da aka yi a ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 1992, domin kalubalanci kasashe daban daban wajen dora muhimmanci kan yawan matalautansu da kuma bambancin ra'ayi da aka nuna musu, da kuma yi kira ga dukkan mutanen duniya da su yi kokarin kubutar da mutane daga kangin talauci.