in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron shugabannin kafofin watsa labaran Sin da Afirka a Afirka ta Kudu
2015-12-02 11:20:04 cri

Kimanin shugabannin kafofin watsa labaran 138 da suka fito daga kasar Sin da kasashen Afirka 47 ne suka halarci wannan taron da aka gudanar jiya Talata a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, inda suka tattauna hanyoyin da suka shafi yadda za a nunawa juna goyon baya da kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za a inganta harkokin watsa labarai da za su dace da matsayin kasa da kasa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Afirka ta Kudu Zuma sun taya murnar bude taron, inda shugaba Xi ya bayyana cewa, ya ji dadin taken taron wato "kago sabbin hanyoyin hadin gwiwa na zamani a fannin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka", ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, hadin gwiwa a wannan fanni tsakanin sassa biyu ya samu babban ci gaba, kuma zai kara habaka nan gaba, yana fatan kafofin watsa labarai na sassan biyu za su kara yawan fannonin cudanya, tare da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu, saboda hakan zai kara karfafa dankon zumunci tsakanin al'ummomin kasashen Sin da Afirka.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, darektan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin Jiang Jianguo ya bayyana cewa, yanzu hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta samu bunkasuwa daga duk fannoni, kafofin watsa labarai su ma sun taka muhimmiyar rawa, musamman wajen kara zurfafa fahimtar juna. Jiang Jianguo ya ce, "Yayin da ake kokarin raya hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, abubuwa mafiya muhimmanci su ne zumunci tsakanin jama'ar sassa biyu, da kuma cudanyar al'adun tsakanin sassa biyu, ana iya cewa, kafofin watsa labarai suna ba da gudumawa matuka."

Don haka, Jiang Jianguo ya gabatar da shawarwari hudu, wato na farko, a kara mai da hankali kan hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, na biyu, a kara zurfafa zumunci tsakanin jama'ar Sin da Afrika, na uku, a yi kokari tare domin bullo da tsare-tsaren da suka dace a fannin watsa labarai, na hudu kuwa, a kara zurfafa cudanya tsakanin kafofin watsa labarai na sassan biyu.

Ministan mai kula da shirye-shiryen raya kasa a fadar shugaban Afirka ta Kudu Jeff Radede shi ma ya yi jawabi yayin taron, inda ya ce, yanzu lokaci ya yi na kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka. Ya ce, "Ina farin ciki matuka da ganin yadda Sin da Afirka ke kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaran sassan biyu, kamata ya yi mu yi amfani da wannan dama mai kyau domin bullo da tsare-tsaren harkokin watsa labarai da suka dace ta hanyar yin hadin gwiwa, ban da haka, ya kamata mu yi hada kai tare domin kara kyautata dangantaka tsakanin kafofin watsa labaran Sin da Afrika, wannan zai taimaka a samu sabuwar dabarar bunkasa sha'anin kafofin watsa labarai yadda ya kamata."

Shugaban gidan talabijin na Najeriya Sola Omole ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, dangantakar sada zumunta bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka ta riga ta shafi fannoni da dama, don haka lokaci ya yi na kara karfafa cudanyar kafofin watsa labarai. Ya ce, "Muna da imani cewa, za mu yi mamaki matuka kan hadin gwiwa tsakanin al'ummar kasar Sin masu kwazo da himma sama da biliyan 1 da miliyan 300 da al'ummar kasashen Afirka sama da biliyan 1, haka kuma ana sa ran hadin gwiwa tsakaninsu zai jawo hankulan jama'ar kasashen duniya. Yanzu haka matsalar da ke shafar fannin watsa labaran kasa da kasa ita ce ta rashin daidaito, amma ina fatan za a magance wannan matsala ta hanyar hadin gwiwa mai zurfi da ke tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka."

Game da batun karfin fada a ji da kafofin watsa labaran kasashen yamma ke da shi kan harkokin rayuwar bil-adam, mataimakiyar shugaban gidan rediyon kasar Sin Li Ping tana ganin cewa, ya kamata Sin da Afirka su kara karfafa cudanya tsakaninsu, inda ta gabatar da shawarar cewa, kamata ya yi a bullo da wani tsarin aiki na hadin gwiwa tsakanin manyan kafofin watsa labaran sassan biyu, saboda hakan zai kara habaka karfin tasirinsu yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China