in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta yi awon gaba da wasu mata a kauyen Bam dake jihar Borno
2015-11-30 21:39:59 cri
Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyen Bam mai nisan kilomita 170 daga Maiduguri fadar mulkin jihar, inda suka hallaka mutane akalla 7, tare da cinnawa wasu gidaje da dama wuta, kafin daga bisani su yi awon gaba da wasu 'yan mata.

Wata majiyar rundunar tsaron kasar ta tabbatarwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua da aukuwar wannan hari na safiyar ranar Lahadi, koda yake mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Borno Victor Ikuku, ya ce basu samu rahoton sace 'yan matan ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China