in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli na FOCAC na farko da za a gudanar a nahiyar Afirka
2015-12-02 12:25:49 cri

Daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Disamba ne za a gudanar da taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a takaice a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu.

An fara taron na FOCAC ne a birnin Beijing na kasar Sin a shekarar 2000, kuma wannan shi ne taro na biyar cikin jerin tarukan dandalin, kana shi ne taron koli na dandalin na farko da za a gudanar a nahiyar Afirka.

Tun lokacin da kasar Sin ta kulla dangantaka da kasashen Afirka, wannan dangantaka take ta bunkasa, abin da ya sa masu sharhi suka bayyana cewa, wannan dangantaka ta yi babban tasiri ga bangarorin biyu, duk da cewa, wasu kasashen yammacin duniya na yi wa wannan kyakkyawar dangantaka bahaguwar fahimta.

Sai dai duk da wannan rashin fahimta da irin wadannan kasashen ke yi wa wannan dangantaka dake tsakanin Sin da Afirka, shugabannin kasar Sin sun jaddada cewa, babban tushen dake tsakanin Sin da Afirka ba zai canja ba.

Alkaluma sun nuna irin tallafi da moriyar da kasashen Afirka suka samu daga wannan dangantaka a bangarori daban-daban kamar su al'adu, ilmi, makamashi, sufuri, tattalin arziki, kiwon lafiya, da dai sauransu. Na baya-bayan nan shi ne shirye-shiryen da kasar Sin ta tsara samar wa nahiyar Afirka da nufin raya masana'antu da bangaren aikin gonanta.

Saboda muhimmancin wannan dangantaka dake tsakanin bangarorin biyu, ya sa aka kafa wannan dandali, abin dake kara nuna karfafa wannan dangantaka mai tarin alheri ga sassan biyu.

Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarori biyu su mutunta alkawuran da suka cimma, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarori gwamnatoci da al'ummomin kasashen biyu. (Ibrahim/ Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China