in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna fata za a samu kwalliya ta biya kudin sabulu a yayin taron kolin FOCAC
2015-12-01 11:09:41 cri

A jajebirin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da za a yi a birnin Johannesburg da ke kasar Afrika ta Kudu, al'ummar Hausawa da ke kasashen Nijeriya, Nijer, Ghana da Kamaru, har da wata 'yar kasar Faransa kuma bahaushiya sun sa ran sosai game da taron.

Abudullahi Ibrahim Mahuta, dan majalisar dokokin jihar Katsina ta Nijeriya ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a dandalin duniya, musamman a nahiyar Afrika, kuma ya ce, kofofin Nijeriya a bude ga kasar Sin, ganin manyan kamfanonin kasar Sin da dama suna gudanar da harkoki a Nijeriya, yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Salou Mahaya, jami'in ma'aikatar kula da makamashi da man fetur na Nijer ya ce, Sin ta taimaka wa jamhuriyar Nijer sosai, musamman ma wajen kafa tashar samar da wuta ta Gurbanda, da gina babban madatsar ruwa ta Kandaji, sun yi amfani ainun wajen raya kasar.

Mohammed Munirou Limuna, Gwamnan jihar yankin arewa na Ghana ya ce, ta hanyar hadin gwiwa da lardin Jiangxi na kasar Sin, jihar yankin arewa na Ghana ya samu ci gaba sosai, yana fata za a ci gaba da hadin gwiwa yasu-yasu.

Maisouna Soumailla, shugaban kamfanin man fetur na Ghana mai suna Nagamne ya ce, yana fatan shugaban kasarsa John Dramani Mahama da shugaban Sin Xi Jinping za su inganta hadin gwiwa tsakaninsu, musamman ma wajen kafa masana'antun hadin gwiwa don samar da guraben ayyukan yi ga al'ummar Ghana.

Garba Innousa, wanda ya samu lambar yabo ta sada zumunta a shekarar 2015, har ya samu jinjinawa daga firaministan Sin Li Keqiang, ya ce, ganin yanzu kamfaninsa na TBEA da gwamnatocin kasar Sin za su kara taimakawa kasar Kamaru da sauran kasashen Afrika wajen samar da wuta, da muhimman ababen more rayuwa, ta hakan, za a samu ci gaba a nahiyar.

Kelle Sam, 'yar kasar Amurka, wadda ta taba yin zama a Jamhuriyar Nijer, ta lankanci harshen hausa, yanzu, tana nazari a jami'ar kasar Faransa, ta ce, Sinawa sun kawo magunguna da dama ga kasashen Afrika musamman ma wajen kashe cutar zazzabin cizon sauro, wanda ya taimakawa nahiyar sosai, yana fatan kasashen Afrika za su koyi fasahohin da Sin ta samu, don samun ci gaba.

Shehu malami Sheriff Ibrahim, manazarci a fannin kasar Sin, ya ce, tunanin da Shugaban Xi ya gabatar na hanyar Siliki, da Ziri Daya Hanya Daya, suna da amfani ainun, sabo da sabbabin tunani ne, kuma zai iya hada kasashen Afrika da ragowar kasashen duniya baki daya. Yana fatan kasar Nijeriya za ta inganta hadin gwiwa da kasar Sin, musamman ma ganin shugabannin kasashen biyu suna da tunanin raya kasa kusan irin guda. Kaman shugaban Xi ya gabatar da tunanin abubuwa 4 na raya kasa, kuma shugaban Nijeriya Buhari shi ma ya yi kokari don yaki da cin hanci da rashawa da farfado da tattalin arziki da yaki da kungiyar Boko Haram, kuma kasashen biyu za su inganta hadin gwiwa a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China