in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron sauyin yanayi na Paris
2015-11-26 17:43:09 cri

Sama da kasashe 190 ne ake sa ran za su halarci taron MDD na shekarar 2015 game da sauyin yanayi da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 11 ga watan Disamban shekarar 2015.

Manufar taron ita ce, cimma wata yarjejeniya a hukumance game da yadda za a magance matsalar sauyin yanayi da ta ki ci ta ki cinyewa.

Wannan dai shi ne karo na farko cikin sama da shekaru ashirin (20) da MDD ke fatan ganin kasashen duniya sun kai ga cimma wata yarjejeniya da za ta kawo karshen wannan matsala baki daya.

A yayin tarukan da aka gudanar a Warsaw a shekarar 2013 da kuma Lima na Peru a shekarar 2014, an amince cewa, dukkan kasashe su gabatar da tsare-tsarensu na rage fitar da iskar da ke gurbata muhalli a taron na wannan shekara.

Masana na cewa, babbar matsalar da ke hana kawo karshen wannan matsala ita ce, ta rashin cika irin alkawuran da manyan kasashe suka yi a tarukan baya dangane da samar da kudi da kuma rage gurbatacciyar iskar da masana'natun kasashen nasu ke fitarwa.

Wannan dai shi ne babban taro da kasar Faransa ta taba shiryawa, kuma ana sa ran mahalarta kimanin 50,000 da suka hada da wakilan gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin MDD da kungiyoyin shiyya-shiyya da na fararen hula ne za su halarta.

Masu sharhi na fatan wannan taro ya kawo karshen abubuwan da ke hana ruwa guda game da matsalar sauyin yanayin duniya da ke shafar kusan dukkan bangarorin rayuwar bil-Adam a duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China