151123-Rancen-kudin-da-wasu-mata-Sinawa-suka-samu-ya-taimaka-musu-cimma-burinsu-na-yaruwa-Kande.m4a
|
Tongren wani gari ne a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Inda wakilinmu ya gamu da wata mace mai suna Yang Li, wadda ta tuka mota zuwa gidan Nie Shuzhen, wani dan karamin kauye da ke bayan garin Heping, bayan da ta gama aikin da ta ke na buga tambarin kayayyaki.
Kamfanin da Madam Yang Li ta kafa ya samu iznin samar da kayayyakin sake-sake masu alamar tambarin "Qinxiu", kuma wannan shi ne dalilin da ya sa Yang Li ta je kauyen Heping, domin daukar matan da suka iya saka. Ita dai Madam Nie Shuzhen manomiya ce mai shekaru 40 da haihuwa kuma ta yi fice ne a fannin shuke-shuke, ta kuma samar wa mata fiye da 60 guraben aikin yi a gonakinta da ke da murabba'in mita dubu 200, hakan ya sa kungiyar matan da aka kafa ke ganawa a gidanta.(Kande Gao)