151120-saya-da-sayarwa-ta-yanar-gizo-lubabatu.m4a
|
Ranar 11 ga watan Nuwamba yanzu haka ya kasance tamkar wani biki ne a nan kasar Sin musamman ga masu saya da sayarwa ta yanar gizo, inda a wannan shekara manyan kamfanonin hada-hadar cinikayya ta yanar gizo sun cimma nasarori masu armashi. Bisa ga kididdigar da aka yi, yawan cinikin da aka yi a wannan rana ta 11 ga watan Nuwamba ya kai kimanin kudin Sin yuan biliyan 91 da miliyan 200, wato cikin sa'o'i 24 ne kawai, adadin da ya karu da kusan kashi 60% bisa na shekarar bara. Domin samun karin haske a kan lamarin, sai a biyo mu cikin shirin.(Lubabatu)