Yayin zantawar tasu, minista Chang ya bayyana cewa, a cikin shekaru 55 da suka gabata, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Mali, kasashen biyu sun gudanar da hadin gwiwa a fannoni daban daban. Ya ce Sin na nuna goyon baya ga kasar Mali wajen kiyaye ikon mulkin kan ta, da cikakken yanki da kuma tsaron kasar. Kaza lika Sin za ta yi biyayya ga manufar da shugaba Xi Jinping ya gabatar kan kasashen nahiyar Afirka, sa'an nan za ta hada kan sauran kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali a Mali cikin dogon lokaci.
A nasa bangare, Tieman Hubert Coulibaly godiya ya yi ga kasar Sin game da goyon baya da taimakon da take baiwa kasar Mali cikin dogon lokaci. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin horar da jami'ai, da kiyaye zaman lafiya a tsakaninsu, tare da sada zumunci tsakanin rundunonin soja na kasashen biyu.(Fatima)