151111-Taron-shugabannin-Afirka-da-Indiya-Sanusi.m4a
|
Firaministan Indiya Nerandra Modi ya ce, an shirya taron ne da nufin bunkasa tattalin arziki, magance matsalar sauyin yanayi, makamashi maras gurbata muhalli, harkokin sufuri, tsarin noma na zamani, dabarun adana ruwa da kasashen nahiyar Afirka. Bugu da kari, Mr Modi ya bayyana cewa, Indiya za ta baiwa kasashen Afirka tallafin dala miliyan 600 don gudanar da ayyukan ci gaba
Masana na kallon taron a matsayin wani kokari da Indiya ke yi na zawarcin kasashen nahiyar Afirka da suka dade suna kyakkyawan dangantaka da kasar Sin domin gudanar da harkokin kasuwanci.
Bayanai na nuna cewa, kasuwancin da ke tsakanin Indiya da Afirka ya ninka zuwa dala biliyan 72 tun daga shekarar 2007, sai dai masana harkokin tattalin arziki na ganin cewa, wannan adadi bai taka kara ya karya ba.
'Yan Afirka da dama ne dai ke zuwa kasar ta Indiya don gudanar da harkokin karatu da neman jinya cikin rahusa, matakan da Indiya za ta kara amfani da su wajen kara bunkasa dangantakarta da kasashen na Afirka.
Sai dai masu fashin baki na cewa, da sauran tafiya kafin a iya tantance makomar wannan dangantaka tsakanin sassan biyu. (Ibrahim/Sanusi Chen)