151104-Za-a-daina-amfani-da-dokar-nan-ta-haifar-da-daya-tilo-a-kasar-Sin-Sanusi.m4a
|
An dauki wannan mataki ne a karshen taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a ranar Alhamis 29 ga watan Otoban shekarar 2015 a nan birnin Beijing.
Wata sanarwar da aka fitar bayan zaman taro karo na 5, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (CPC) na 18 da aka fara tun a ranar Litinin 26 ga watan na Oktoba, ta bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne don daidaita ci gaban al'ummar tare da magance matsalar karancin matasa da kasar ke fuskanta.
Tun a karshen shekarun 1970 ne aka kaddamar da shirin tsara iyali a kasar, inda aka baiwa iyalai mazauna birane damar haifar da daya tilo, kana 'ya'ya biyu ga iyalan da ke yankunan karkara, idan har suka haifi 'ya mace. Daga bisani kuma aka sassauta wannan doka, ta yadda iyalai za su iya haifar da na biyu, idan har dukkan iyalan su kadai ne a wajen iyayensu.
Bugu da kari, an sassauta wannan doka a watan Nuwamban shekarar 2013, bayan zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS na 18.
Za a fara amfani da wannan doka ce da zarar ta samu amincewar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a watan Maris na shekara mai zuwa.
Masana na bayyana cewa, wannan matakin da mahukuntan kasar ta Sin ta dauka ya zo a dai-dai lokacin da ya dace, kana zai taimakawa kokarin kasar na zurfafa yin gyare-gyare daga dukkan fannoni. (Ibrahim/Sanusi Chen)