151028-zaman-rayuwar-dalibin-nijer-bako.m4a
|
Mohammed Warim, wani dalibin da ya fito daga jihar Damagaram ta jamhuriyar Nijer, duk da cewa, shi ba bahaushe ba, amma tun daga ya yi karatu gami da girma a jihar Tawa ta kasar, ya lakanci wannan harshe sosai, yayin da yake karami, ya dinga kallon fina-finan kasar Sin, yana sha'awar zuwa karatu a kasar Sin, kuma a bara, burinsa ya cika, ya zo birnin Shanghai don koyon harshen Sinanci, sannan a bana, Allah ya ba shi damar karatu don neman digiri na farko a lardin Gansu na kasar Sin, yana fata zai ci gaba da ba da gudummawa ga kasar Sin da jamhuriyar Nijer, bayan da ya kammala karatu gine-gine a kasar Sin.(Bako)