151028-An-fidda-sakamakon-rahoto-game-da-jirgin-saman-Malaysia-da-ya-fado-a-gabashin-Ukraine-Sanusi.m4a
|
Kamfanin kera rokoki samfurin Buk mai suna Almaz-Antei na Rasha da kwamitin bincike kan hadarin jirgin sama na Ukraine suma sun fidda nasu rahotannin, inda suka zargi juna da haddasa hadarin jirgin saman na Malaysia.
Jirgin saman fasinjan na Malaysia mai lamba MH17 ya taso ne daga birnin Amsterdam a kan hanyarsa ta zuwa birnin Kuala Lumpur,dauke da mutane 298, ciki har da 'yan Holland kimanin 196 kuma dukkan fasinjojin sun mutu.
A cikin rahoton binciken, ba a ambaci wanda ya harba rokar ba, amma an nuna cewa, wurin da aka harba roka da ke gabashin kasar Ukraine yana karkashin ikon dakarun dake adawa da gwamnatin Ukraine ne .Binciken da ita ma Rasha ta yi, ya nuna cewa, sojojin gwamnatin Ukraine ne suka harba rokar.
Masu fashin baki na cewa, kamata ya yi tun farko hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta duniya ta hana zirga-zirgar jirage a yankin da ake tafka riciki,amma ba a yi hakan ba har lokacin da hadarin ya faru. Yanzu dai koma mene ne, masana na cewa, ko ba dade gaskiya za ta fito fili. (Ibrahim/Sanisu Chen)