in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musayar al'adu tsakanin Sin da Birtaniya ta samu babban sakamako
2015-10-23 12:51:59 cri

An ce, kyautata zumunci tsakanin jama'a yana da muhimmanci yayin da ake kokarin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kuma musayar al'adu hanya ce mafi dacewa yayin da ake kokarin zurfafa zumunci tsakanin jama'ar kasashe daban daban. Yanzu dai, ana iya cewa, musayar al'adu tsakanin Sin da Birtaniya ta riga ta shiga wani sabon matsayi.

Joe Haniff, daya ne daga cikin daliban Birtaniya dubu 6 wadanda ke karatu a kasar nan Sin. Ya zo Beijing ne a watan da ya gabata domin koyon Sinanci a jami'ar Qinghua. Joe Haniff ya ce, yana son koyon Sinanci ne domin ya kara fahimtar al'adun kasar Sin, hakan zai taimaka masa wajen samun aikin yi a nan gaba. Ya ce, "A ganina, banbancin tsarin karatu a kasar Sin da Birtaniya shi ne daliban Sin sun fi nuna kwazo da himma wajen yin karatu, kuma abubuwan da suke koyo suna da yawa. Idan har zan samu aiki a kasar Sin, to, ina ganin zan yi aiki a nan."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, ana kara samun 'yan Birtaniya da ke sha'awar koyon Sinanci, yanzu haka akwai kwalejin koyar da Sinanci ta Confusius guda 27 a kasar, adadi mafi yawa a kasashen mambobin kungiyar tarayyar Turai EU. Sakataren kudin Burtaniya George Osbone ya ce, nan da shekarar 2020, yawan daliban da za su koyi Sinanci zai karu zuwa dubu 5 a Birtaniya.

A sa'i daya kuma, daliban kasar Sin masu yawan gaske su ma sun je Birtaniya domin yin karatu.

Yu Jiayi, dalibar kasar Sin da ta taba zuwa jami'ar London koyon manufar jama'a tana ganin cewa, ta fi son yadda ake koyarwa a Birtaniya. Ta ce, "A jami'ar Birtaniya, mu kan je dakin karatu don neman takardun da muke bukata bayan mun kammala daukar darasi a aji, in ba haka ba, ba za mu ci jarrabawa ba. Kuma daliban da suka zo daga kasashe daban daban sun fi son su tattauna da takwarorinsu ba tare da wani shamaki ba."

Bisa kididdigar da aka yi, ya zuwa karshen shekarar 2014, yawan daliban kasar Sin da suka zo Birtaniya karatu ya kai dubu 150.

Hakazalika, hadin gwiwa tsakanin Sin da Birtaniya a fannin kafa makarantu shi ma ya karu, ya zuwa watan Aguntan bana, yawan makarantun da Sin da Birtaniya suka zuba jari tare a kasar Sin ya kai 17, ayyukan da abin ya shafa sun kai 240.

Kan wannan, ministan ba da ilmi na kasar Sin Yuan Guiren ya bayyana cewa, hadin gwiwar harkokin ba da ilimi zai kawo babban tasiri ga hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Ya ce, "Ba ya ga kara karfafa cudanya a fannin ba da ilimi, tsarin zai kuma kawo moriya ga dalibai, sannan zai kara habaka tushen sada zumunta tsakanin kasashe biyu cikin dogon lokaci. Matasa su ne kashin bayan ci gaban ko wace kasa, don haka kamata ya yi a kara mai da hankali kan aikin ba da ilmi ga matasa, musamman ma a fannin cudayar al'adun kasa da kasa."

Ban da shirin ba da ilmi, Sin da Birtaniya suna gudanar da hadin gwiwa a fannoni daban daban, misali kimiyya da fasaha, al'adu, wasannin motsa jiki, kafofin watsa labarai, kiwon lafiya da dai sauransu.

Farfesa a cibiyar yin nazari kan huldar kasa da kasa ta zamani ta kasar Sin Chen Fengying ta bayyana cewa, kara zurfafa musayar al'adu tsakanin Sin da Birtaniya zai ingiza dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. Ta ce, "Yayin da ake gudanar da hadin gwiwa a fannin al'adu, abu mafi muhimmanci shi ne a hada al'adun gabashin duniya da na yammacin duniya ta hanyar da ta dace, ta yadda zai kasance al'adun duniya. Cudanya tsakanin Sin da Birtaniya wani bangare ne kawai, kuma zai kara kyautata hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da hulda tsakaninsu yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China