in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Birtaniya sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin samar da lantarki da makamashin nukiliya
2015-10-22 13:38:54 cri

Rukunin cibiyoyin samar da lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya na Guangdong na kasar Sin wato CGN da kuma rukunin cibiyoyin samar da lantarki na kasar Faransa sun kulla yarjejeniya game da zuba jari kan tashar samar da lantarki da makamashin nukiliya ta Hinkley ta C a yankin Somerset na Birtaniya. Wannan alamace da nuna cewa, kasar Sin ta fara gudanar da sha'anin samar da lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin nukiliya a kasuwannin kasashen duniya da suka ci gaba. Masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, wannan aikin tamkar zakaran gwajin dafi ne ga sauran ayyukan da za a yi a nan gaba, kuma dukkannin bangarorin biyu za su ci moriyar shirin, sannan wannan shirin zai nuna wa kasashen duniya sabuwar fasahar samar da lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta kasar Sin.

Tashar Hinkley tana Somerset dake kudu maso yammacin Birtaniya, ita ma sabuwar tasha ce da aka gina a kasar tun bayan shekaru 20 da suka gabata, tashar za ta iyar samar da lantarki kashi 7 cikin dari na bukatun kasar. A watan Satumban bana, ministan kudin kasar George Osbone ya taba kai ziyara a kasar Sin, inda ya sanar da cewa, gwamnatin kasarsa za ta samar da kudin lamani kimanin fam biliyan 2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3 da miliyan dari daya ga yarjejeniyar gina tashar. Ma'aikatar kudin Birtaniya ta ce, matakin da gwamnatin kasar ta dauka zai bude kofa ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Birtaniya a fannin gina tashar samar da lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin nukiliya.

Bisa yarjejeniyar da aka kulla, rukunin kasar Sin zai mallaki hannun jarin kashi 33.5 cikin 100 na tashar, yayain da rukunin Faransa zai mallaki kashi 66.5 cikin 100. Bangarorin biyu za su zuba jari tare domin kera na'urorin samar da lantarki da makamashin nukiliya iri na Turai guda biyu a tashar, an ce, yawan kudin da za a bukata a matakin farko zai kai fam biliyan 18 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 28.

Shugaban cibiyar yin nazari kan makamashi ta jami'ar Birmingham ta Birtaniya kuma masanin makamashin nukiliya Martin Forel ya yi bayani cewa, hadin gwiwar zai taimakawa sha'anin kirkire-kirkiren na'urorin makamashi masu inganci na kasar Sin da ya shiga kasuwannin kasashen waje. Ya ce, "Wannan wata dama ce mai kyau ga kamfanonin kasar Sin inda za su kara fahimtar kasuwar lantarkin da aka samar ta hanyar makamashin nukiliya a Birtaniya. Idan sun gano halin bunkasuwar lantarkin makamashin nukiliya da kasar ke ciki, to, tashar da za su gina za ta kasance babban aiki a matsayin misali."

Game da dalilin da ya sa Birtaniya ta zabi kasar Sin da ta shiga wannan aiki, mataimakin babban manajan rukunin masana'antun nukiliya na kasar Sin Yu Peigen ya gaya wa manema labarai cewa, lamarin ya shafi bangarori biyu wato Birtaniya tana fama da matsala wajen samun jari, ban da haka kuma fasahar samar da lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta kasar Sin tana da inganci sosai.

A kwanakin baya ne, rukunin makamashin nukiliya na kasar Sin da cibiyar gwajin makamashin nukiliya ta kasar Birtaniya suka sanya hannu kan "Hadaddiyar sanarwa game da kafa cibiyar yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Birtaniya wajen yin nazari kan makamashin nukiliya", hakan ya nuna cewa, kasar Sin ta fara gudanar da hadin gwiwarta tare da kasashen da suka ci gaba a fannin fasahar makamashin nukiliya mai inganci.

Mataimakin babban manaja rukunin masana'antun nukiliya na kasar Sin Yu Peigen ya ce, "Lamarin na da babbar ma'ana, saboda shi ne karo na farko da bangaren Birtaniya ya zuba jari kan wata hadaddiyar cibiyar yin nazari, baki daya bangaren Birtaniya zai samar da kudi fam miliyan 25 a cikin shekaru 5 mazu zuwa."

Kan wannan batu, farfesa a cibiyar yin nazarin huldar kasa da kasa ta zamani ta kasar Sin Chen Fengying tana ganin cewa, kulla yarjejeniyar zai kara ingiza sha'anin kirkire-kirkire na kasar Sin ta yadda zai iya shiga kasuwannin kasashen waje. Ta ce, "Faransa da Sin sun zuba jari tare a Birtaniya, lamarin ya shaida cewa, kamfanonin kasar Sin da na kasashen da suka ci gaba suna iya gudanar da hadin gwiwa yadda ya kamata, hakan ya nuna cewa, kamfanonin Sin suna iya shiga kasuwannin kasashen da suka ci gaba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China