in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya jaddada muhimmancin cudanya da juna da taimakon juna a tsakanin kasashen Sin da Birtaniya
2015-10-21 14:46:52 cri

 


Da misalin karfe hudu na yammacin jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da matarsa Madam Peng Liyuan sun isa babban ginin majalisar dokokin Birtaniya, inda shugabar majalisar dattijan Birtaniya Boroness Frances D'Souza da shugaban majalisar wakilai John Bercow suka musu kyakkyawar karba. Bayan da shugaba Xi ya shiga babban dakin ba da lacca, dukkan 'yan majalisun biyu na tsaye, domin karrama su.

A madadin dukkan majalisun biyu na Birtaniya, shugaban majalisar wakilai John Bercow ya yi jawabi don yi wa shugaba Xi Jinping lale marhabin da ziyararsa a Birtaniya da kuma zuwa majalisar dokokin kasar. A nasa jawabin, shugaba Xi ya fara ne da cewar yana da kyakkyawar fatar wannan ziyara tasa zuwa Birtaniya akwai matukar alheri kuma ga alama ziyarar ta wannan karo za ta ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. Ya kara da cewa,

"Yau shi ne yini na farko da na iso kasar Birtaniya don ziyarar aiki bisa gayyatar da sarauniya Elizabeth ta biyu ta yi mini. Ko da yake ban jima da isowa ba, amma na fara jin annashuwa saboda irin dangantakar da ke tsakanin Sin da Birtaniya, tare da kuma zumunci dake tsakanin jama'ar kasashen biyu. Don haka ina fatan alheri ga yadda ziyara ta a wannan karo za ta ciyar da dangantaka tsakanin kasashen biyu gaba."

Bugu da kari, shugaba Xi ya jaddada cewa, ko da yake akwai nisa a tsakanin Sin da Birtaniya, amma suna jawo hankulan juna cikin dogon lokaci. Tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, huldar dake tsakanin kasashen biyu ta samu babban ci gaba a fannoni daban daban wadda ba a taba ganin irinta a tarihi ba. Yana mai cewa,

"Birtaniya kasa ce ta farko a yammacin duniya da ta amince da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, baya ga kyakkyawan jagoranci wajen kafa dangantakar daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashe membobin kungiyar EU. Sa'an nan Birtaniya tana kan gaba wajen musayar kudin RMB bayan yankin HongKong, baya ga yadda ta zama kasar da ta fi jawo yawan dalibai Sinawa tare da kafa kwalejin Confucius mafi yawa a cikin kasashe membobin kungiyar EU. Har ila yau ita ce kasa ta farko a yankin Turai da ta yi amfani da kudin RMB wajen samar da rance, sannan ta zama kasa ta farko a yammacin duniya wajen neman shiga bankin zuba jari kan muhimman ababen more rayuwa a nahiyar Asiya. Duk wadannan abubuwa sun tabbatar da cewa, Sin da Birtaniya na cikin yanayi na cin moriya juna."

Ban da wannan, Shugaba Xi ya ce, dangantaka a tsakanin Sin da Birtaniya ta samu ci gaba ne sakamakon fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen biyu da goyon bayan juna da kuma zumuncin dake tsakanin kasashen. Zamanin da muke ciki yanzu, zamani ne da ke dora muhimmanci kan zaman lafiya da bunkasuwa, kana zamani ne da ya kamata kasa da kasa su hada gwiwa don magance matsaloli da samar da ci gaba. Sakamakon haka, lokaci ya yi da Sin da Birtaniya za su kara rike hannayen juna wajen karfafa dangantakar a tsakaninsu daga dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare-tsare a nan gaba.

Bayan da shugaba Xi ya kammala jawabinsa, 'yan majalisun biyu na Birtaniya sun yi masa tafi sosai. Daga bisani Madam D'Souza, shugabar majalisar dattijan Birtaniya ta yi jawabinta don nuna godiya dangane da ziyarar da ya kawo kasar da kuma ba da laccar. Madam D'Souza ta ce,

"Sakamakon kara fahimtar juna, za mu iya inganta hadin kanmu a fannonin ilmi, kimiyya, al'adu, wasanni, da kuma ciniki, musamman ma game da wasu ayyukan masu alaka da aikin ilimi da na al'adu da na kimiyya. Tabbas ne za mu samu kyakkyawan sakamako. Shugaba Xi, ziyararka ta nuna muhimmancin hadin kan kasashenmu, muna farin ciki da zuwanka kasarmu. Na yi imanin cewa, dukkanmu za mu karu sosai ta ziyararka a wannan karo."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China