in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin ziyarar shugaban kasar Sin a kasar Burtaniya ga kasashen duniya
2015-10-21 12:49:19 cri

A ranar Litinin 19 ga watan Oktoban shekarar 2015 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga nan birnin Beijing zuwa kasar Burtnaiya don fara ziyarar aiki mai matukar muhimmanci, ziyarar da masana ke cewa, za ta bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin sassan biyu.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na bayyana cewa, bana shekara ta 11 ke nan da kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Birtaniya. Saboda haka firaministan kasar Birtaniya Mista David Cameron yana daukar wannan shekara a matsayin shekara mai muhimmanci ta kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2. A saboda haka ne ma shugaba Xi na kasar Sin ya zabi wannan lokaci domin ya kai ziyara kasar Birtaniya bisa gayyatar sarauniya Elizabeth ta biyu.

A yayin wannan ziyara ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su fito da wani sabon tsari kan dangantakar da ke tsakaninsu, tare da bullo da sabbin muradu da shirye-shirye. Matakan da ake gani za su taimaka wajen karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin 2 a nan gaba.

Bayanai na nuna cewa, Burtaniya ta zama kasa ta biyu a kungiyar EU wajen saka jari da cinikayya a kasar Sin, Yayin da ita kuma kasar Sin ta kasance kasa ta biyu wajen yin cinikayya da kasar Burtaniya.

Yanzu haka kuma, kasar Burtaniya na tsara wani shiri na kyautata muhimman kayayyakin more rayuwa da raya cibiyar tattalin arziki da ke yankin arewacin kasar da ma sauran manyan tsare-tsare raya masana'antun kasar, wadannan ra'ayoyi sun yi kama da shirin nan na "Ziri daya da Hanya daya" da kuma raya harkokin kirkire-kirkire kafin shekara ta 2025.

Bugu da kari, kasar Sin ta kafa cibiyar banki tantance kudin kasar Sin na RMB a birnin London, kuma Burtaniya ta zama kasa ta farko da ke sayar da hannayen jari da RMB a kasashen yammacin duniya, sannan kasa ta farko da ta sanya kudin Sin cikin kudaden ajiyar kasar, wannan ya kasance muhimmin abin da ke jawo hankalin hadin gwiwar bangarorin biyu.

Masu fashin baki na fassara ziyarar a matsayin wadda za ta kara bunkasa hadin gwiwa a fannonin al'adu, makamashi, hada-hadar, kudi, ilimi, cinikayya, fahimta da mutunta juna da sauransu ba ma ga kasashen biyu ba har ga duniya baki daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China