151021-za-mu-koyi-fasahohi-bako.m4a
|
Abubakar Jibril Haruna, wani dan kasuwa da ya dinga kaiwa da dawowa tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, yana aiki a kamfanin kayayyakin Citex na Nijeriya, ya zo kasar Sin don sayen atamfa da yadudduka, ya ce, saboda kayayyakin Sin suna da araha, kuma akwai inganci, shi ya sa, kullum su kan zuwa Sin don odar wasu kayayyaki. Ya ce, idan ya nuna zane-zanen kabilar Hausa ko ta Fulani ko ta Yarabawa ga masu sayar da kayayyaki na kasar Sin, cikin mako guda ko makwanni biyu, za a samu irin tufafin kabilar Hausa ko ta Fulani kamar yadda hausawa suka yi su. Ya ce, yanzu, a karkashin shugabancin Alhaji Habibu Abdulahi Mohamud, kamfanin Citex yana son inganta hadin gwiwa da kasar Sin, don koyon fasahohi daga kasar Sin, sannan za a raya sana'ar sassaka ko dinkin tufafi a Nijeriya.(Bako)