151016-Tuyouyou-lubabatu.m4a
|
A ranar 5 ga wata, cibiyar nazarin kimiyyar likitanci ta Karokinska dake kasar Sweden ta sanar da cewa, Madam Tu Youyou, 'yar kasar Sin ta raba kyautar Nobel ta likitanci tare da dan kasar Irland William Campbell da kuma Satoshi Omura dan kasar Japan kan taimakon da suka bayar na gano wata sabuwar hanyar maganin zazzabin cizon sauro.
To, shin me ya sa aka ba ta wannan babban yabo, kuma wane gudummawa ce sinadarin nan na Artemisinin zai bayar? A biyo mu cikin shirin, domin samun karin haske.(Lubabatu)