A ranar Talata da ta gabata ne, masu bincike suka fidda sakamakon bincike a kasar Holland, inda suka yi imani cewa, roka samfurin Buk ce ta yi sanadiyyar hadarin jirgin saman. Game da wannan, a ranar laraban nan 14 ga wata, Rasha ta nuna tsayayyiyar adawa game da wannan. Wani jami'in ma'aikatar zirga-zirgar jiragen saman Rasha ya ce, rahoton da Holland ta bayar, ya wuce gona da iri.
A ranar 17 ga watan Yulin shekarar bara, jirgin sama mai samfuri MH17 da ya taso daga Amsterdam a kan hanyarsa ta zuwa birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia, ya fadi a yankin gabashin kasar Ukraine da ke kusa da kan iyaka da kasar Rasha, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 298 dake cikin .(Bako)